Gwamnan Kano ya bukaci gwamnatin Edo ta biya diyyar kashe matafiya 16



Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya buƙaci Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo da ya tabbatar da biyan diyyar mafarauta da aka kashe a jiharsa ta Edo a hanyarsu ta komawa gida domin bukuwan Sallah.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da gwamna Monday Okpebholo ya jagoranci tawagar gwamnatinsa zuwa Kano domin jajantawa gwamnati da al'ummar jihar bisa abin da ya faru na kisan matafiyan a makon jiya.

A jawabinsa, gwamna Abba ya yaba da ƙoƙarin gwamnan na jihar Edo bisa matakan da ya ɗauka, inda ya ce a nasu ɓangaren sun ɗauki matakan da suka dace domin hana ramakon gayya, "domin mutanen Kano masu son zaman lafiya ne da maraba da baƙi .

"Yawancin waɗanda aka kashe ɗin ƴan Kano ne. An tare su ne a jiharka a hanyarsu ta dawowa daga Fatakwal, aka gana musu azaba, sannan aka ƙone wasu daga cikinsu."

Gwamna ya kuma yaba da ƙoƙarin gwamnatin Edo wajen ganin an ɗauko gawarwakin tare da binne su kamar addini ya tsara, da kuma kama waɗanda ake zargi.

Sai dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce yana buƙatu biyu da yake so gwamnan ya yi ƙoƙarin ganin an cika su.

A cewasa, "muna so a gabatar da waɗanda ake zargi a gaban menama labarai domin duniya ta gansu kowa ya ga fuskokinsu. Wannan zai taimaka wajen kwantar da hankalin iyalan waɗanda aka kashe," in ji shi.

Ya ƙara da cewa Gwamnan na Edo ya faɗa cewa masa za a tabbatar da hukunci, "kuma ina da tabbacin gwamna zai cika wannan alƙawarin."

Ya ce,"abu na biyu shi ne muna so a tabbatar da biyan diyyar waɗanda aka kashe ɗin ga iyalansu. Na san kai mutum ne mai nagarta da cika magana, kamar yadda ka ce za a biya diyya, muna so a biya diyyar cikakkiya, kuma a cikin lokaci."

Tun da farko, gwamna Monday Okpebholo ya bayyana takaicinsa kan yadda al'amarin ya faru, inda ya ce tuni an kama mutum 14 da ake zargi suna da hannu a lamarin kuma za su tabbatar da sun fuskanci hukunci.

Bayan ganawarsu a fadar gwamnatin jihar, Gwamna Abba ya jagoranci Gwamna Okpebholo zuwa ƙaramar hukumar Bunkure domn jajantawa iyalan waɗanda aka kashe.

Okpebholo ya shaidawa iyalan cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba har sai an tabbatar da adalci.

Post a Comment

Previous Post Next Post