Rundunar ƴansanda a jihar Oyo ta ce ta gano wata ƙungiya da ke safarar mutane a Ibadan, babban birnin jihar.
Ƴansandan sun ce sun ceto mutum 83 haɗe da wani yaro a wani gida a yankin Orogun da ke Ibadan, inda ake kyautata zaton an ajiye mutanen na tsawon lokaci, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.
Binciken farko da aka gudanar, ya nuna cewa mutanen ƴan asalin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo ne - waɗanda aka shigo da su zuwa Najeriya kan yaudarar cewa za a sama musu ayyukan yi.
Ana kuma zargin cewa ɓata-garin sun karɓi kuɗaɗe dala da yawa a hannun iyayen waɗanda suka yi safararsu.
Yanzu dai mutanen da aka ceto suna hedkwatar ƴansandan jihar ta Oyo da ke Ibadan, inda hukumomi ke ci gaba da yin bincike domin gano ƙarin masu hannu a lamarin.
Post a Comment