Sister KI DUBA ALHERIN DA ZAI ZO Idan Mijinki Ya Kara Aure!!!


Daga Fatima Adamu Tinja Fika, jihar Yobe


Wata mace tana ganin karin aure a matsayin matsala, amma idan ta duba da kyau, za ta iya fahimtar cewa Kishiya na iya rage mata nauyin ayyuka, taimaka mata a rayuwa, ko zama aminiya. Kada ki saurari tsegumin mutane, domin wasu mutane suna amfani da karin aure don É—aura wa mace damuwa. Za su iya cusa mata bakin ciki da rashin kwanciyar hankali. Don haka ki yi kokarin guje wa tattaunawa da mutanen da ke karfafa miki badin ciki, sai dai ki nemi mafita daga waÉ—anda ke da hikima da fahimta.

Ki kara wanzar da soyayyarki da mijinki, a maimakon ki shiga gunaguni da rashin jin daÉ—i, ki yi kokari ki kula da mijinki, ki karfafa soyayyarku, kuma ki ba shi girmansa. Mace da ke da kyakkyawan hali da tausayi tana iya samun karin gata a wajen mijinta fiye da wacce ke nuna fushi da damuwa.

Ki nemi lada a wajen Allah. Hakika hakuri da karbar kaddara na da babban lada a wajen Allah. Idan kika rungumi karin aure da zuciya É—aya, Allah zai sanya albarka a rayuwarki, kuma ya kara miki daraja. Idan kika ci gaba da kyautata hali, Allah zai ba ki farin ciki a zuciyarki fiye da abin da kike tsammani.

Saboda haka, karin aure na iya zama kalubale, amma idan mace ta fahimci hikimar Allah, ta guji tunanin banza, ta yi hakuri, ta dage da ibada, kuma ta kula da kanta, za ta fi samun farin ciki da kwanciyar hankali. Aure ba gasa ba ne, kuma mijinki ba zai daina kaunar ki ba saboda Kishiya. Ki mai da hankali kan yadda za ki ci gaba da rayuwarki cikin nasara da jin daÉ—i.

 KARIN AURE NAUYI, ADALCI, DA HAKKIN NAMIJI A MUSULUNCI.

Ina kira ga mazan da suke kokarin karin aure kan adalci a lokacin neman aure, bayan sun yi aure, da kuma a cikin zamantakewa da matansu:

1. Yin Adalci Tun Kafin a Kara Aure

Idan kana shirin kara aure, ka tabbatar da cewa dalilinka na da inganci kuma kana da karfin nauyin iyali fiye da É—aya. Kada ka kara aure kawai don kwaÉ—ayi ko son zuciya, sai dai don neman alheri da yardar Allah. Ka tattauna da matar gidanka cikin hikima da tausayi, kada ka cutar da ita da boye-boye ko rashin fahimtar da ita da kyau.

A lokacin neman mace, kada ka yaudari sabuwar matar da ce mata ba ka da aure ko ka boye gaskiya kan halin da kake ciki. Ka bayyana wa matar farko game da shirin ka cikin ladabi da tausayi, ka fahimtar da ita cewa karin aure ba ya nufin kiyayya ko raguwar kauna. Kada ka jefa kanka cikin halin da ba za ka iya cika hakkokin aure ba. Ka duba kanka, shin kana da ikon kula da mata biyu daidai ba tare da zalunci ba?

Bayan ka yi karin aure, ka tabbatar da gida ba ya rushewa saboda karin aure. Kada ka nuna wa matar farko raini ko rage mata daraja. Ka bi dokokin Allah wajen rabon dare, kulawa da hakkokin matanka, da kuma guje wa son zuciya. Kada ka bari sabuwar soyayya ta rufe maka ido, ka manta da matar farko wacce ta yi zaman aure da kai tun farko. Ka zama mai tausayi da hakuri.

KAMMALAWA

Karin aure babban nauyi ne da ke bukatar adalci, hikima, da tsoron Allah. Maza su tabbata suna da ikon kula da mata fiye da É—aya ba tare da zalunci ba. Mata kuma su fahimci cewa Allah ne Ya halatta karin aure, kuma su nemi lada da kwanciyar hankali maimakon rikici.

Idan an yi karin aure da adalci, zai zama albarka ga iyali da al'umma. Idan kuwa aka yi shi da zalunci, zai zama fitina da rushewar gida. Allah Ya ba mu ikon tafiyar da aure bisa tafarkin shari'a da soyayya.

Post a Comment

Previous Post Next Post