Yadda ‘Yar Shekara Saba’in Ta Yi Walimar Saukar Alkur’ani Mai Girma A Kano



Malama Rabi Muhammad, daya ce daga cikin daliban makatantar Alkur'ani a Kano da suka yi walimar saukar Alkur’ani mai girma a makon da ya gabata. Wakilinmu ya samu zantawa da ita. Ga yadda tattaunawar ta kasance.


FMB PRESS HAUSA: Za mu so ki gabatar da kanki?


Suna na Rabi Muhammad.


FMB PRESS HAUSA: Shekarunki  nawa?


Shekaruna saba’in (70).


FMB PRESS HAUSA: Kina daya daga cikin daliban da suka yi walimar saukar Alkur’ani mai girma. Duk da shekarun ki, ga shi kin yi sauka. Me ya ba ki himma?


Ka san karatunmu na da, idan ka yi karatun ba ka kai Sabbi ba ma, sai a cire ka a yi maka aure. Ni da aka yi min aure, yaron gidan da muke haya a gidan shi ke biya min karatuna. Muna yi tare har muka taso muka dawo Kawo lokacin Maitatsine. Sai na samu almajiri dan karami ya rika koya min. Da kuma yarinyata Maryam Malama ce, kodayaushe ita ma tana koya min. Idan sun je makarantar Malam Musa Maradi suka dawo, abin da suka yi nima sai na rika yi. Sai ta zama ita ce Malama ta. Na koya mata dan bokon da na sani, ita kuma tana koya min Arabi. Haka muka rika yi. Ina so na ci gaba da karatu, to Maigidan nawa ka san al’ada sai a ce matan aure ba za su yi karatu ba, sai na samu wannan yarinyar ta wa Maryam, kungiyarsu sai aka ce a kawo ‘scholarship’, shi ke nan da Allah ya taimake ni ka ga na girma na yi. Amma da da na ke matashiya maigidan nawa yana kishi ko sannu ba zai bari na yi wa wani ba, sai ya hana ni karatun. To amma da yake na tsufa sai ya hakura. Ni ko na yi ta murna na shiga wannan makaranta. Shi ne fa Allah ya sa na kammala.


FMB PRESS HAUSA: Ga shi yau kin yi saukar Alkur’ani, ya kike ji a ranki a matsayinki mai shekaru saba’in a duniya?


Wayyo Allah. Tunda saukar nan ta zo nake farin ciki nake jin dadi. Jiya ma tunda muka farka ban yi bacci ba, ina ta farin ciki. Wannan taro da aka yi shi, ka ga tunda na yi shi shi ke nan Alhamdulillah, Sai kuma dan abin da na samu a hadda mun dunga zuwa ke nan kafin mu bar duniyar.


FMB PRESS HAUSA: Akwai Dattawan da suke ganin sun girma da ilimi, wane kira kike da shi zuwa gare su?


Shi wannan karatu za mu samu lada ne da yawa. Domin samari da ‘yan mata da yake karatun a da ya daina, yanzu gani na haka da ya yi sai ka ga idan Allah ya yi da rabo sai ya dawo ya ci gaba da karatun.


FMB PRESS HAUSA: Mene ne sakon ki ga al’umma?


Muna musu fatan alheri. Don Allah, don Annabi su dage suma su koyi karatu. Ba a tsufa da karatu. 

Post a Comment

Previous Post Next Post