SHEIKH DR. AHMAD ABUBAKAR GUMI YA GABATAR DA MUHADARA A GARIN BOMO



Daga Mardiyya Kabiru

A ranar lahadi data gabata 23/02/2025 ne Dr. Ahmad Gumi ya samu damar kawo ziyara ga Al'ummar dake  garin BomO. Ya fara magana akan Menene Muhimmancin Mazhabar Malikiyya a wannan zamanin da Muke ciki  muna Karshen zamanine yanzu, fatan kowa yasan hakan. MANZON Allah(S) yace za ai makaryata masu karkatar da mutane daga kan gaskiya sunkai 30 kuma kowanne su zaice shima Annabi ne anayi masa wahayi. 

Yanzu muna wani zamanin da shaidanun duk sun bayyana Inda suka dauke mutane kuma suka Karkatar da musulmai a hanya musulunci da kuma sun kawar da musulmai daga sunan MANZON Allah (s). Masu zuwa da abinda zasu raba kan Al'ummar musulmai yakamata kafin ayi aiki dashi dole sai an duba shin Al'qurani ne yazo dashi koko sunnah ta kawo hakan koko magabata sukace ayi to idan ba,a samu daya daga cikin wadannan bane yazo dashi to wajibi ne abarshi. Akwai wani malamin daya bude baki zaka gane wannan malamin na kwarai ne ko bana kwarai bane dan haka sai wanda Allah ya tseratar Sannan zai iya tsallake hakan zaka iya ganin ferfesa ko babban malami amma ya bace baya hanyar Sunnar manzon Allah(s) Yanzu zamanin da muke ciki shine na banbantu duba da yadda idan kahau kafar sadauwar zakaga malamai suna ta maganganu a kafar sadarwa wanda keda karamin fahinta daganan saisu canza mashi tinani ya sauka akan sunnar manzon Allah(S). Dan haka Kada kabi mutum Dan Allah ya bashi harshe fasahan da zai rinka magana Aa kabishi ne saboda abinda yake fadi idan gaskiya ne. Daga cikin jahadin daya Kamata muyi shine zamu iya tashi mu shiga kauyuka muna fahintar dasu menene abinda Sunnar Manzon Allah(s)a daina cutar su da maganar Daba gaskiya ba shima idan munyi hakan jahadi ne. Kadan ke nan daga cikin jawabin da ya yi.  


FMB Press Hausa


Post a Comment

Previous Post Next Post