Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana bada wannan sanarwan a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa Jami’an gidajen yari da kuma sojjin HKI suna dukan kawo wuka kan falasdinawa da suka shiga hannunsu, sannan suna azabtar da su sosai, daga ciki har tare da yanke yanke wasu gabban jikinsu.
Kungiyar ta kara da cewa, mutum yana iya ganin alamun duka da kuma kumburan wurare da dama a jikin Falasdiwa. Banda haka Falasdinawan da aka saka, sun bayyana cewa bayan duka da kuma azabtarwa sojojin HKI sukan hana magunguna ga wadanda basa da lafiya har wasunsu su rasa rayukansu.
Rahoton ya kara da cewa wadannan shaidun sun tabbatar da cewa, HKI tana aikata laifukan yaki, a kan al-ummar Falasdinu sannan alamu sun nuna cewa Falasdinawa da dama sun rasa rayukansu a gidajen yari k kuma wauraren da yahudawan suke tsare da su. Sannan HKI tana buye duk wata shaida da suke tabbatar da irin mummunar mu’amalan da suke yi da Falasdinawa.
Post a Comment