Wata babbar kotun jihar Jigawa ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin kisa da gangan. Alƙalin kotun ta huɗu wadda ke zamanta a Dutse, babban birnin jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya, Mai shari'a Ahmed Mohammed Abubakar ne ya yanke hukuncin bayan kammala shari'ar.
Ya ce kotun ta sama Hamim Auwalu da Ashiru Salisu na ƙauyen Sabalari da ke ƙaramar hukumar Dutse da laifukan haɗa baki, da yaudara da garkuwa da mutum domin karɓar kuɗin fansa, da kuma kisa da gangan. An kama su ne bisa laifin kashe wani mai suna Tahir Adamu Hassan a ranar 4 ga watan Afrilun 2024 a ƙauyen Sabalari, bayan lauyan mai ƙara ya gabatar da shaidu huɗu, waɗanda suka gabatar da shaida da ke tabbatar da laifn waɗanda ake zargi.
Suma waɗanda ake ƙara sun gabatar da shaidu guda biyu. Bayan sauraron jawaban ɓangarorin biyu ne, alƙalin kotun Mai shari'a A.A Abubakar ya tabbatar da laifin waɗanda ake zargi, waɗanda ya ce laifukansu sun saɓa wa sashe 96 da 97 na kundin laifukan penal code na jihar. Kotun ta kuma ce ta tabbatar da laifin waɗanda ake zargi na kisa da gangan. Don haka ne kotun ta yanke hukuncin zaman gidan yari na shekara ɗaya ga waɗanda ake zargi bisa laifin garkuwa, da kuma kisa ta hanyar rataya saboda kisa da gangan.
Sai dai kotun ta bayyana cewa ta lura waɗanda ake zargi sun nuna damuwa tare da da-na-sanin abin da suka aikata, amma "dole hukunci ya yi aiki," kamar yadda sanarwar da hukumar shari'ar Jigawa, wadda daraktan watsa labarai da tsare-tsare, Abbas Rufai Wangara ya fitar. "Wannan hukuncin ya zama kashedi da tunawatarwa cewa shari'a ba za ta amince da aikata laifuka ba, kuma duk wanda ya yi laifi, zai fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata." In ji sanarwar.
Post a Comment