Manjo Janar Hossein Salami, babban kwamandan dakarun kare juyin juya hali, ya tabbatar da cewa shugaban Amurka Donald Trump ya gane hakikanin ikon Iran.
Ya ci gaba da cewa "Trump a zaman farko na shugabancinsa da ya gabata ya fahimci irin karfin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi a kan hakikanin gaskiya, kuma ya yi daidai, kasancewar Iran ba ta yi rauni ba, sai dai ta kara karfi, kuma hakan ya bayyana ga kowa a yau."
Post a Comment