JAGORA (H) YA YI WALIMA TARE DA IYALAN SHUHADA

 

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da misalin karfe 8:00 na dare, a ranar Juma’a 24 ga watan Rajab 1446 (24/1/2025) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gana da sashen iyalan Shahidan Harka Islamiyya a gidansa da ke Abuja.

A yayin ganawar wadda ta kunshi walimar cin abinci tare da iyalan Shahidan a jajibarin ranar taron tunawa da Shahidan Harkar Musulunci na bana, Jagora (H) ya gabatar da takaitaccen tunatarwa a matsayin abincin ruhi ga mahalartan.

Shaikh Ibraheem Zakzaky ya fara da bayani dangane da gangan jiki da kuma rai, da bayyana alakarsu. Yace: “rai din nan ya malala ne a cikin jikin mutum, kuma shi kamar wani haske ne wanda aka malala shi, wanda ido ba zai ganshi ba, amma yana nan. Abin da yake faruwa a wajen mutuwa shi ne ran ne ake cirewa, in aka cire rai to sai gangan jiki ya zama bashi da rai, to shi ne kuma dole a haka rami a bizne shi.” 

Yace: “To kowanne yana da abinci, shi gangan jiki yana rayuwa ne da cin abinci da abin sha, shi kuma dabi’ansa yana son hutu, don yakan gaji. Shi kuma rai da ke malala a gangan jikin nan, shi ma yana da nasa abincin, shi kuma yana rayuwa ne da ilimi da tuna Allah (zikiri), wato ayyukan da suke damfara shi da Allah Ta’ala, su suke raya shi.”

Ya cigaba da cewa: “Kowannensu mutum yana bukatarsa. Za ku ga wasu mutane sun cigaba ta fuskacin gangan jikinsu, amma ransu sun yi baya, saboda ransu ya rabu da Allah. Kuma rai in ya rabu da Allah yakan dinga damun gangan jiki ne, sai mutum ya yi ta mafarke-mafarke yana firgita, ya yi ta wasu miyagun abubuwa, saboda ruhinsa baya samun natsuwa, don natsuwar rai sai in ya damfara da Allah Ta’ala. 

“To su mutane da yawa sukan kula da gangan jikinsu ne, su manta da ransu. Su ne wadanda suka manta Allah, Allah Ya mantar da su kawukansu. Sai ya zama su abin da ya dame su wanka da wanki ne, da cin abinci mai dadi da sauransu, amma in ana musu maganar me kuka yi tanaji don lahirarku, ba su san da lahirar ba, kawai suna sharholiyarsu ne su hole su ji dadi. Su ne masu cewa iyakan rayuwa kawai a mutu shikenan. Amma wadanda suka san cewa akwai rai a cikinsu, shi kuma ran nan yana da nasa abincin, shi ne ma su a ranar gobe kiyama.

“Shi wannan gangan jikin da nake ba ku bayani, shi ne in mutum ya mutu an bizne shi, to shi ran nan da aka ciro, shi ran baya mutuwa, in aka cire shi ana sama da shi ne, lokacin tashin kiyama sai a dawo da shi ran, sai a taso da gangan jikin, bayan gangan jiki kilama ya zama kasa, an saka shi a kasa ya rube, ruwan ya tsotse, kasusuwan ma sun zama kasa sun murkushe, to amma ruhi yana nan. To watan watarana lokacin da Allah Ta’ala ya so ta da mutane, to sai ya ta da jikkunansu, sai rayukan su fito suna yawo kamar fari, sai su je duk inda gangan jikin mutum ya tsiro, ranshi in ya zo sai ya hadu da shi.”

Jagora bayyana yadda shi Shahidai ba kawai za a raba jikinsa da ransa ya jira sai ranar tashi sannan ya hadu ba ne. Yace: “shi Shahidi an yi masa alkawari na musamman, shi nan take yana barin wannan duniyar zai tsinci kansa ne a Aljanna da wani jikin na daban.”

Da yake magana da iyalan Shahidan, Jagora ya yi addu’ar Allah Ya albarkaci rayuwarsu da albarkacin jinanen iyayensu da aka shekar, tare da tsawaita ta, da kuma fatan Allah Ya sa su za su dauki fansa daga azzaluman da suka kashe iyayensu. 

Yace: “Ko badade - ko bajima zalunci ba ya dawwama, za ka ga azzalumi yana ta abinda yake yi, amma ba shikenan ba, watan-watarana abin da suke kokari su hana za su ganshi. Abin da suke ta yunkuri shi ne kar addini ya dawo ya zama shi ke da iko da al’umma. Su abin da suke so su hana kenan, wannan kuma ba zai hanu ba. Ko badade - ko bajima, addinin Allah zai dawo, kuma zai zama jinainan shahidai ne zai raya wannan addini, sakamakon shekar da jinanen nasu ne addini zai dago.” 

Shaikh Zakzaky ya bayyana shahidi a matsayin mai riban duniya da ta lahira, inda yace tun a duniya ana tunawa da shi, sannan kuma yana cikin kyakkyawan makoma a lahira, a yayin da azzalauman da ke kisan kai tun a duniya sunansu ke wanzuwa a matsayin tsinannu, kuma a Lahira su shiga mummunan makomai. 

Yace: “Azzaluman har yanzu ba sun dandara ba ne, su kullum tunaninsu shi ne shekar da jini, ba su da wani tunani sai wannan. To amma mu gaba ta kai mu, saboda gwadamu ake yi. Ko ba a kashe mutum ba zai mutu. Da mai kisan da wanda aka kashen duk watarana sai labari, duk za a zo a wuce kamar yadda muke karanta labarin wadanda suka wuce a baya, muma nan gaba za a karanta labarinmu mun riga mun wuce ne. Amma me? Sunan mutanen kirki yana nan zai wanzu da kyakkyawan Ambato. Sannan sunan miyagun bayi shi me zai wanzu da mummunan suna.”

A nan ne Jagora ya jaddada bukatar kara kaimi wajen tunawa da Shahidai da raya ambatonsu da kuma girmama iyalansu. “Yana da kyau ya zama kowane gari su ma suna alfahari da Gwarazansu - Shahidansu, ya zama suna tunawa da su.” Inda ya bayar da misalin yadda a Jamhuriyar Musulunci kusan kowane gari da suke da shahidai suke saka hotunan Shahidan garin a farkon garinsu da sauran nau’ukan girmamawa ga Shuhada da iyalansu masu girma. Yace: “suna alfahari da shahidan garinsu ne, saboda jinanen wadannan Shahidan shi ya kawo wannan gagarumin nasara da aka samu. Kuma suna girmama iyalan Shahidai.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana nasarar juyin Musulunci a Iran a matsayin abin da azzaluman mahukuntan nan kasar ke jin tsoron aukuwar irinsa, inda ya jaddada cewa: “abinda suke ta jin tsoron nan zai auku fa. Kuma zai auku din! Sun ki ko sun so, kai ma sun ki din! Amma zai auku, don alkawari ne na Allah. Allah Ta’ala ya yi alkawarin zai dawo da addinin nan, kuma addinin nan sai ya dawo. Amma sai an dake an daure.”

Ya karkare da kira ga iyalan Shuhada akan su rika yi ma iyayensu addu’a, da yawan tunawa da su, da addu’ar daukar fansar Allah akan makiya. Yace: “Kuma a yi addu’ar cewa kar jinanensu ya tafi a kawai, Allah Ya dawo mana da addininmu, abin da suka bayar da jinanensu akai ya zama ya dawo insha Allahu Ta’ala.”

@SZakzakyOffice

#MartyrsDay 

#PrayForPalestine 

#OurMartyrsOurHeroes 

25/Rajab/1446

25/01/2025

Post a Comment

Previous Post Next Post