JAGORA (H) YA GABATAR DA ZAMAN JUYAYIN SHAHADAR IMAM KAZEEM (AS)


Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da yammacin ranar Asabar 25 ga watan Rajab 1446 (25/1/2025) ne Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabi dangane da shahadar Imam Musal Kazeem (AS), a gidansa da ke Abuja.

Jagora ya kawo tarihin gwagwarmayar Imam Kazeem (AS) da yadda ya sha fama da sarakunan lokacinsa har zuwa lokacin da sarki Haruna, wanda suke kira Rashid ya ciyar da shi guba a dabino ta hannun wani bafadensa Bayahude mai suna Sindi bin Shahiq.

Yace: “Shi Imam Musa bai musu laifin komai ba, illa kawai shi mai yawan ibada ne, ya tsaya kyam, kuma zukatan al’umma na tare da shi. Kuma wannan ne abin da (azzalumai) basu so, suna son al’umma zukatansu ya zama tare da mahukunta ne, in suka ga zukatan al’umma na tare da wani, wannan sai ya zama barazana a wajensu, sai su ce an yi gwamnati a cikin gwamnati.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa; “In ka bi tarihi za ka ga shi Shahidi akan kala masa wani laifi ne a fake da shi sai a cutar da shi. Amma laifin (kowane Shahidi na hakika) shi ne ya tsaya kyam a tafarkin Allah. Wannan kuma shi ne laifin Shahidanmu.”

Da yake bayani dangane da ranar Shahidan Harkar Musulunci, Shaikh Zakzaky ya bayyana taron “Yaumu Shuhada” na bana a matsayin karo na 35 da fara yinsa a kowace shekara. Yace, zaman farko da aka yi kan tuna Shahidai ya auku a daidai watan Rajab ne, “sai kuma muka ga ai ma ya dace da lokacin shahadar Imam Musal Kazeem, sai kuma muka ga lallai Shahadar Imam Kazeem (AS) kyakkyawan ramzi ne na nuna shahidi ba laifin komai yake ba illa tsayawarsa da ibada ga Allah Ta’ala.”

Jagoran ya karkare jawabinsa da yin magana da dabakokin mutane daban-daban da suka hada da Shahidai da iyalansu, da sauran ‘yan uwa, da sauran al’umma ‘yan zura ido, da kuma azzalumai masu aukar da shahada.

Ga Shahidan da suka bayar da jinanensu a tafarkin Allah, Jagora (H) ya nanata musu cewa: “Ya ku Shahidai, muna taya ku murna da cewa Allah Ta’ala Ya karrama ku da wannan matsayi na Shahada, domin dama mutuwa al’ada ce… Allah Ta’ala Ya karrama ku da wannan matsayi na Shahada a tafarkin wannan addini da kuma bin tafarkin Amirulmuminin (AS) da ‘ya’yansa tsarkaka, wanda shi ne tafarkin Sahibul Asr waz Zaman (ALF).”

Ya kara da cewa: “Kamar yadda ba mu manta da ku a addu’o’inmu ba, wannan ma rana ce da muka dauka domin tunawa da ku, ku ma muna fata ya zama baku manta da mu ba, ku yi ta mana addu’a har mu riski inda kuke.”

Ya kara ba Shahidan tabbaci kamar yadda ya saba da cewa: “abin nan da kuka ba da rayukanku a kai, ba zai tafi kawai ba. Jinainanku su ne za su shayar da bishiyar kafuwar wannan addini daram, kamar yadda ya zama sadaukarwar na farko shi ya wanzar da wannan addinin, sadaukarwar na yanzu ne zai cigaba da wanzar da shi. Shahadarku karfafa mana guiwa ya yi, kuma muna tare da ku, muna jinjina muku, muna fatan Allah Ta’ala Ya bamu guzurin zuwa inda kuke.”

Har ila yau, Jagora ya yi kira ga makusantan Shahidai akan juriya da dakewa a tafarkin Allah, tare da tunawa da Shahidai da koka rashinsu amma ba tare da yin raki ba. 

Sannan ya yi kira ga sauran ‘yan uwa akan bukatuwar mu dake akan tafarkin da Shahidanmu suka bayar da rayukansu a kansa. Yace: “Su masu aukar da shahada abin da suke fata shi ne za su tsorata mu ne. To akwai wata shekara a Yaumus Shuhada, ina magana da mutanen gari ne ba da ‘yan uwa ba, nake cewa, to jama’ar gari, ko kun ga ana baku tsoro da bude mana wuta don kar ku shigo cikinmu, to mu ma yanzu muna baku tsoron, kar ku shigo cikinmu, in kuka shigo za a iya kashe ku, duk wanda baya son a kashe shi kar ya shigo cikinmu.”

Ya jaddada cewa: “In dai har kana so ka rayu kar a kashe ka to kar ka shigo cikinmu, domin mu (azzalumai) suna farautanmu ne ko yau ko gobe, ko da wane lokaci za a iya shahada, saboda haka sai in ka shirya cewa kai ko yau ko gobe za ka iya tafiya, to kai ne namu. Amma in kana ganin a’a’a, to ka sauka lafiya, randa ka shirya ka zo.”

A nan ne Jagora ya yi kira ga ‘yan zura ido akan su zo a yi addini tare da su tun kafin lokaci ya kure musu. Tare da baiwa azzalumai tabbacin rugujewarsu da tabewa da asarar duniya da lahira in ba su daina cutar da masu addini ba. Ya ja hankalin su da cewa: “hakkinku ne akanmu mu tunatar da ku cewa, ita rayuwar nan fa ba dauwama take ba, gidan gwaji ce, an dora mu a doron kasa ne don a gwada mu, a ga wane ne zai kyautata aiki, wane ne kuma zai munana, akwai sakamakon masu kyakkyawan aiki, akwai sakamakon masu mummunan aiki.”

Yace: “Ku tunda kuka dauka ma kanku abin da kuka dauka ku kisa za ku yi, naku kenan! Ku yi kisan, ku rasa mulkin, ku rasa ranku. Kuma ba shi kenan ba, kuma gobe kiyama ku tsaya gaba ga Allah. Amma mu baku taba bamu tsoro da mutuwa ba! Saboda mun san dama karshen kowannenmu ne, ba wanda zai dauwama a nan.”

Ya karkare da godiya ga Allah Ta’ala akan ni’imar dora mu akan hanya madaidaiciya, tare da addu’ar samun sabati gare mu, da kuma karban shahadar Shahidai, da ba da lafiya ga marasa lafiya, da mafita ga wadanda ake tsare da su a kurkukun azzaluman kasar nan.

@SZakzakyOffice

#MartyrsDay 

#PrayForPalestine 

#OurMartyrsOurHeroes 

25/Rajab/1446

25/01/2025

Post a Comment

Previous Post Next Post