Dangote ya karya farashin man fetur



Matatar mai ta Dangote ta karya farashin man fetur daga Naira 950 zuwa Naira 890 kan kowace lita a yammacin wannan Asabar. 

Babban jami’in kasuwanci da yaɗa labaran Matatar Dangote, Anthony Chiejina, ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar yau Asabar. Sanarwar ta ce rage farashin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai ya faɗi a kasuwar duniya. 

Chiejina ya ce rage farashin zai inganta tattalin arzikin ’yan Nijeriya ta hanyar rage musu raɗaɗin tsadar makamashi. 

Ya ƙara da cewa, Matatar za ta ci gaba bitar farashin lokaci zuwa lokaci daidai da yanayin kasuwa kamar yadda ta yi ƙarin farashin makonni biyu da suka gabata. 

Kazalika, sanarwar ta buƙaci dillallai da ’yan kasuwar man fetur da su tabbatar talakawan ƙasar sun rabauta da wannan ragi da aka yi a yanzu.

Post a Comment

Previous Post Next Post