JAGORA (H) YA GABATAR DA JAWABIN ‘RANAR MAB’ATH’



Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da yammacin Litini 27 ga watan Rajab 1446 (27/1/2025) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabin ranar ‘Mab’ath; wato ranar da aka fara wahayi ga Manzon Allah (S) da nufin isar da sako ga talikai, a gidansa da ke Abuja.

Jagora ya bayyana ranar ‘Mib’ath’ a matsayin muhimmiyar rana ce a wajenmu. Yace: “A wajen Amah suna cewa rannan ne Manzon Allah (S) ya yi Mi’iraji zuwa sama. (Da yake) su a wurinsu sau daya Manzon Allah ya yi mi’iraji zuwa sama. (Alhali) mu kuwa muna da ruwaya da ya nuna mana cewa, Manzon Allah (S) ya yi mi’iraji zuwa saman bakwai sau 120. Saboda haka ba sau daya ya je saman bakwai ba, tana iya yiwuwa daya daga cikinsu ya zama ranar 27 ga watan Rajab ne.”

Yace, ranar ‘Mib’ath’ na nufin randa aka ce yanzu an yarda Manzon Allah (S) ya isar da sako. “Wato kamar ‘officially’ an ‘commission’ din shi, an ce daga yau an ayyanaka a matsayin Manzo zuwa ga mutane, isar da sako.” Ya kara da cewa: “Amma tambaya; dama can shi Manzon Allah ne? Eh! Eh! Ehh! Tun dama can shi Manzon Allah ne. Tun ma kafin a yi halitta yake Manzon Allah.” 

Jagora ya cigaba da cewa: “Lokacin da Allah Ya halicce shi ya halicci Manzon Allah ne, lokacin da Ya sa haskenSa a Adam Ya sa hasken Manzon Allah (S) ne, Ya rika jujjuya shi daga tsarkakakken uba zuwa tsarkakakkiyar uwa, har Ya kai shi ga tsarkakakken uba; Abdullahi Alaihis Salam, da tsarkakakkiyar uwa; Aminatu Bintu Wahab (AS), har ya zuwa lokacin da ya fito (aka haife shi). An haifi Annabi ne, ya girma Annabi ne, amma ba a yi mashi izini ya kira mutane ba, sai da ya cika shekara 40, sannan aka ce to yanzu fada wa mutane sako.”

Ya jaddada cewa ba a ranar ‘Mib’ath’ ne ya zama Annabi ba, dama Annabi ne shi. Yace: “Shi ne fiyayye a cikin dukkan Annabawa, fiyayyen cikin Manzonni, shi ne Manzo da ya zo a karshe, amma shi ne shugabansu duka. Kuma sakonsa kawai ce mafita ga dukkan al’umma duniyarsu da lahirarsu.”

Yace: “Manzon Allah (S) shi ne na farko a jerin Annabawa, amma na karshe a aikowa. Shi aka aiko daga karshe, amma shi ne farkonsu a Annabta. Bihasali ma muna iya cewa, duk sauran Manzonni, sun zo sun isar da sakonsa ne kafin isowarsa. Wannan shiri ne na Allah Ta’ala.”

Jagora ya yi bitan yadda aka kirkiri wasu labarurruka akan yadda farkon saukan wahayi ya kasance, don a rage matsayin wannan Annabi (S), inda ya warware su da bayanai gamsassu a cikin jawabin da ya gabatar na tsawon kimanin awanni uku.

Ya jawabinsa da addu’ar samun jinkan Allah Ta’ala gare mu, da iyayenmu, da iyayen iyayenmu, da malamanmu, da Malaman malamanmu. Da kuma addua ga Shahidai da masu rauni, tare da fatan mafita ga wadanda suke tsare a hannun azzalumai a kurkukun Kuje, da Keffi da sauran guraren tsarewan soja da ‘yan sanda da jami’an tsaron ciki, wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba.

@SZakzakyOffice

#YaumuMabath 

#PrayForPalestine 

#OurMartysOurHeroes 

27/Rajab/1446

27/01/2025

Post a Comment

Previous Post Next Post