Daga Mansur Kabir
A ranar Lahadi ne 12/01/2025 aka yi bikin yaye dalibai masu koyan sana'oin hannu kamar su; throwing pillow, takalma, man shafawa, turare da sauran su a makarantar Royal Crown Global Entrepreneur a babban zauren taro na Balarabe Tanimu.
Taron ya samu halartar manyan mutane kamar su Sadaukin Zazzau Alhaji Yusuf Shehu Idris inda ya yi jawabai masu ratsa jiki da jawo hankalin matasa wurin neman sana'oin domin inganta rayuwar su da kuma karfafa gwiwa waje neman ilimi. Sannan sai jawabin tarihin makarantar daga bakin Daraktan Makaranta Abubakar Dan Masani inda ya kawo tarihin a takaice sannan ya baiyana dalilan sa wajen samar da wannan makarantar.
Sai Kuma jawaban shugaban karamar hukumar Sabon Gari Sheikh Jamilu Albani Samaru shima ya nuna farin cikinsa wajen dagewa da wannan dalibai suka yi waje koyan sanar dogaro da kai. Sai kuma gabatar da wasan kwaikwayo daga daliban makarantar mMai taken suna KUKAN KURCIYA. Daga karshe sai kuma baiyana kayayyakin da wannan dalibai suka hada da kansu. An yi taro lafiya an tashi lafiya.
Post a Comment