Taron Kungiyar Tsoffin Daliban Bomo (BOSA)


A ranar Asabar 4/1/2025 wannan kungiya mai suna a sama ta gabatar da taron da ta saba yi lokaci bayan lokaci domin ganin yadda za a ci gabantar da wannan makaranta da daliban cikin ta zuwa gaba, Taron ya samu halartan tsofaffin dalibai da dama ciki harda wadanda aka fara bude makarantan tare da su. 

Sannan an tabo bangaren matsalolin da makarantar ke da shi musamman bangaren ‘laboratory’ inda aka tattauna yadda za a gyara shi ya ci gaba da aiki a rinka amfani dashi. 

Sannan aka bada shawarwarin cewa lallai dalibai su nemi sana'a kar a tsaya akan karatu kawai lallai a hada biyu. Sannan abin burgewa a wannan taron shine an hada zoom wanda ko baka samu halarta ba zaka iya neman link kayi joining, kuma alhamdulillah ya samu halartan mutane da dama da sassan kasannan. 

A karshe an rufe taron da addua da fatan alkhairi.


@Media forum bomo

Post a Comment

Previous Post Next Post