An Yi Jana’izar Marhuma Malama Fatima Bintu Abdullah



A ranar Litinin 16/12/2024 ne aka yi jana’izar Marhuma Malama Fatima (Binta) Abdullahi (Babbar Matar Shaikh Yakub Yahya Katsina ) wadda ta rasu a ranar Lahadin da ta gabata (15/12/2024), bayan fama da doguwar jinya ta tsawon shekara 7. 

Shaikh Yakub ne da kansa ya jagoranci jana’izarta da yi mata sallah, inda ɗaruruwan ’yan’uwa Musulmi maza da mata daga sassa daban-daban na ciki da wajen garin Katsina, suka rakata zuwa makwancinta na ƙarshe da ke maƙabartar Ɗan’Marna. 

An yi mata shaida da kyawawan ɗabi’u da kuma karamci, sannan ta kasance ma’abociyar karatun Al-ƙur’ani hatta a halin jinyar da take.  Marhuma Malama Binta dai ’yar’uwa ce ta jini ga Shaikh Yakub Yahya (mijinta) kuma ta rasu ta bar ’ya’ya 12,  jikoki 34 sai tattaɓa kunne 5.

Post a Comment

Previous Post Next Post