A ranar Talata ne 'Yan uwa Almajiran Sayyed Zakzaky (H) na garin Kurmi a Majalisin Bomo suka shirya gagarumin Maulidin Manzon Allah (SAWW) wanda suka saba shiryawa duk shekara. Bayan bude taro da addu'a, sai karatun Alkur'ani mai girma. Daga nan kuma wakilin 'yan'uwa na Samaru ya yi takaitaccen jawabi akan Manzon Allah (SAWW).
Daga nan sai Babban Malami mai jawabi Malam Ahmad Maiwada Zariya ya fara da gwalagwalan jawabi akan tasirin da maulidi yake da shi ga al'ummar musulmai. Inda yake cewa bai kamata al'ummar musulmai su dauki ranar da aka haifi Manzon Allah ( SAWW) a matsayin ranar da ba na murna ba domin da zuwansa ne duk wani Rahma ya sauka.
Ya ci gaba da cewa; Manzon Allah shi ya zo mana da Alkurani kuma ya aikata Alkur'ani din a aikace a zahiri. Manzon Allah (SAWW) shi ne addinin musulunci saboda duk abin da addini ya zo da shi a wajen Manzon Allah (SAWW) za a kwaikwaya a wajen Annabi Muhammad Rasullulah. Daga karshe kuma ya yi mana albishir da cewa indai muka bi koyarwar Manzon Allah (SAWW), to duk wahalar da muke ciki za ta zo karshe.

Post a Comment