Tare Da MLS. Abduljalal Muhammad
Lafiya shi ne jigo a rayuwar kowacce halitta musamman mutum Dan Adam a duk lokacin da mutum ya kasance yana da isashen lafiya to zai samu damar da zai yi rayuwa cikin aminci da kuma kuzari ba tare da samun tangardan karfin jiki ko kuma yanayin rashin jindadin jiki ba. To shin me yasa yanzu cututtuka suke yaduwa fiye da ashekarun baya?
Hakan na faruwa ne sakamakon yawan 'chemicals' a cikin abubuwan cin mu da shanmu sabanin baya komai munacin 'natural' ne kuma a ka'ida kowanne abu yana da abin da muke kira (indication) sannan yana da (effect) ma'ana kowanne abu yana da amfanin shi kuma yana da illarsa karamin misali shi ne bari mu dauki magani 'PARACETAMOL' kowa ya san wannan maganin kuma kila zamu iya cewa kowa ya san amfaninsa- to shin mun san illarshi (CONTRA INDICATION)?
To illar 'paracetamol' shi ne 'Hypertitis' ma'ana ciwon hanta duk wanda yake yawaita shansa ba bisa ka'ida ba, to ya kan haifar da ciwon hanta. To haka 'chemicals' din da suke cikin abincinmu da shanmu wajibi ne mu kula da abubuwan da suke da 'over chemicals' misali tun daga magin da muke amfani da shi a abinci da sauran abubuwan dake dauke da 'chemicals' mu tabbatar mun kiyaye ka'idonjin aiki da su. Zamu dan tattauna akan hanyar da za mu kula da lafiyarmu (prevention).
Matakin farko shi ne tsaftar jiki da kuma tsaftar muhalli:
Shi tsafta yana tainakawa sosai wajen kaucewa daukar kwayar cuta misali cutar (maleria parasite) cutar cizon sauro akasari sauro yafi zama a gurin da yake da yawan ciyawa (grass) ko kuma inda yake da yawan kwata. To wajibi ne mu zama masu tsaftace kwatan Unguwanninmu ko gidajenmu da kuma cire duk wata ciyawa saboda a cikin ciyawa ko kwata sauro yake kyankyasan kwayayan halittansa (Incubation period) don haka mu tabbatarda tsaftace wadannan abubuwan da muka lissafo domin gujema kamuwa ta cututtuka.
Sai kuma tsaftar jiki shima yana tainakawa sosai misali tafin hannun Dan Adam da kuma wasu bangare na jikin shi suna daga cikin bangarori mafiya hatsari wajen kamuwa da cuta anaso a kowacce rana mutum yazamto akalla ya yi wanka sau biyu; na farko da safe idan ya tashi sai kuma da daddare idan ya gama ayyukansa hakan zai taimaka wajen kawar da wasu kananun cututtuka da kan iya zama a saman fatan Dan adam.
Sai kuma uwa uba tsaftar makewayi da kuma rijiyoyinmu akwai abin da akasarin mutane ba su gane ba a wannan fagen shi ne (underground connection) ma'ana kawance tsakanin makewayinmu da rijiyoyinmu shin mun san cewa duk wanda bai ba da tazaran mita 20 tsakanin makewayi da rijiya ba akwai yiwuwar haduwar bayangida da ruwan shan sa?
To lallai dole mu tabbatar makewayinmu ba shi kusa da rijiyanmu saboda hakan na haifar da cututuka mara misaltuwa misali amai da gudawa (cholera) ko kuma yawan samun masu 'typhoid fever' a gida daya ba tare da an san musabbabi ba. Insha Allah a takaice ke nan nan gaba zamu dauko cututtukan sannan mu tattauna yadda za a magance su.
Na ku a kullum MLS Abdul Jalal Muhammad Bomo.

Post a Comment