Daga Abban Hydar
Shaikh Bukhari Sambo Bomo ya fara magana ne akan muhimmancin neman ilimi akan matasa wanda ya ce wannan ilimin kuwa ya hada da boko da bangaren addini. Sannan ya kara da cewa; matasanmu su zamo suna da fahimtar juna a tsakaninsu da mutane gari wajen kyautata alakarsu domin ganin sun fahimci kiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).
Sannan ya ce akwai bukatar matasanmu su zamo masu bauta ga Allah da barin duk wani abin da Allah ya haramta a aikata shi. Sannan ya ja hankalin matasa su kasance masu neman na kansu masu sana'a domin su dogara da kansu domin kaucewa shiga halaka.
Sannan ya karfafi matasa akan tsayawa a tafarkin gwagwarmaya; “mu tsaya kyam babu gudu babu ja da baya”, duk a cikin jawabin da Shehin Malamin ya yi. Daga karshe Malam Murtala ya kara jawo mana hankali sosai akan tsayawa kyam a gwagwarmaya.

Post a Comment