TUNAWA DA WAKI'AR 1 GA WATAN RABI'UL AWWAL - Daga bakin Sheikh Bukhari Sambo Bomo

 


Shehin Malamin wanda ya dawo gida Nijeriya daga Iraqi hutu ya yi bayani ne akan abin da ya gani da idonsa zahiri a Hussainiyya Bakiyyatullah da gidan Jagora Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) a Gyallesu a lokacin waki'ar Buhari ta shekarar 1436. 

Shehin Malamin a cikin bayaninsa ya bayyana cewa; kamar yadda muka sani ranar 12/12/2015 daidai da 1/1/1436 wanda ya yi daidai da ranar da za a canja tuta a Hussainiyya Bakiyyatullah daga na juyayin shahadar Imam Hussain zuwa na farin ciki da haihuwa Manzon Allah (SAWW).  

Ya ce; cikin mamaki da rana tsaka azzalumar hukumar Sojojin Nijeriya ta afkama 'yan'uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a Hussainiyya Bakiyyatullah da Gidan Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) da Darur Rahmah wato makabartan shahidai dake Dembo da sauran muhallan 'yan'uwa a Zariya. 

Inda gwamantin ta dauki nauyi shan jinin 'yan'uwa musulmai da hannunta wajen kisa, kamu, cirewa sisters hijabai, kona mutane da rai wannan kadan ne daga cikin abin da azzalumai suka aikata akan 'yan'uwa musulmai.  Sannan ya kara da mana bayani akan  yadda ya ga waki'ar a Hussainiyya har zuwa lokacin da ya baro Hussainiyya ya dawo gidan jagora a Gyallesu.

Post a Comment

Previous Post Next Post