Dandalin 'Trustee, Mobilization Awareness' ta yi bikin yayen dalibanta karo na biyu a ranar Lahadi 29/9/2024.
Taron an yi shi ne a Balarabe Tanimu Dake IAR na Jami'ar
Ahmadu Bello dake Zariya. Taron na yayen daliban da suka koyi sana'o'in dogaro
da kai kamar dinki, koyon abinci, gyaran wuta, da sauran su. Taron an fara shi
ne da misalin karfe 10:00 na safe.
Daga cikin manyan bakin da suka samu halartar taron sun hada da; Sarkin Bomo Alhaji Muktar Salihu
wanda ya hada da wakiltar Hakimin Basawa da Bomo.
Sai Sarkin Hayin Dogo Samaru, Wakilin Hon. Sadiq Ango
Abdullahi, Wakilin Sanatan Shiyya ta daya, Chiroman Bomo Alhaji Abubakar
yariman Bomo, Kansilar Gundumar Bomo Isiya Barista, Wakilin Hon. Jamilu
Abubakar Albani, Dahiru Mangal da sauran manyan baki.
Taron bayan gabatar da jawabai da alkawura an kuma gabatar
da bayar da takardar shaidar kammalawa ga dalibai maza da mata.

Post a Comment