N-HYPPADEC Ta Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Da Jihar Kaduna, Ta Kai Ziyara Masarautar Lere


Daga Awwal Umar Kontagora

Manajan Darakta kuma Babban Jami'in Hukumar Raya Yankunan Masu Samar da Wutar Lantarki ta Ƙasa (N-HYPPADEC), Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa, ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwar hukumar zuwa Masarautar Lere a Jihar Kaduna domin ƙarfafa haɗin gwiwa da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki wajen bunƙasa ayyukan ci gaba.

Ziyarar, wadda aka gudanar a ranar 4 ga Agustan 2026, ta biyo bayan taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a ranar 3 ga Agusta, inda aka tattauna kan buƙatun ci gaba da ƙalubalen da al'ummomin yankin ke fuskanta.

A yayin ganawar da suka yi da Mai Martaba Sarkin Lere, Engr. Suleiman Umar, an tattauna kan hanyoyin inganta rayuwar al'umma, ƙarfafa ayyukan raya ƙasa da kuma bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin N-HYPPADEC, masarautu da al'ummomin yankin.

Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa ya jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da suka dace da buƙatun al'ummomin yankunan da ke ƙarƙashinta, tare da tabbatar da gaskiya, riƙon amana da ci gaba mai ɗorewa.

Ya kuma bayyana cewa sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar ayyukan ci gaba, saboda haka hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da su.

A nasa jawabin, Sarkin Lere ya yaba wa N-HYPPADEC bisa ƙoƙarinta na inganta rayuwar al'umma da kuma yadda take tuntuɓar sarakunan gargajiya kafin aiwatar da ayyukanta.

Bayan ganawar, tawagar hukumar ta ziyarci aikin gina sabon sashen 'yan sanda da ake yi a Masarautar Lere domin ƙarfafa tsaro. An bayyana cewa aikin ya kai kusan kashi 70 cikin 100 na kammalawa, kuma N-HYPPADEC ta yi alƙawarin tallafa wajen kammala shi cikin gaggawa domin fara amfani da shi.

Haka kuma, tawagar ta kai ziyara zuwa Kogin Lere, wanda ke cikin Kogin Kaduna, domin duba barazanar da kwararar ruwan kogin ke yi wa gadar da ta haɗa hedikwatar Masarautar Lere da sauran al'ummomin da ke makwabtaka da ita.

Hukumar ta ce wannan rangadi wani ɓangare ne na shirinta na rage haɗarin ambaliya da zaizayar ƙasa, tare da kare rayuka, dukiyoyi da inganta juriyar al'umma ga sauye-sauyen yanayi.

Post a Comment

Previous Post Next Post