Hauza da jami'a ba cibiyoyin da ke bayar da takardar shaidar karatu kawai ba ne. A'a, su ne masana'antun gina tunani mai 'yanci, dasa kyawawan ɗabi'u, da kuma ba wa mutum gogewar rayuwa da za ta sa ya zama mai amfani ga al'umma tare da ba da gudummawa wajen ci gabanta.
Malaman hauza da jami'a, da kuma malamai a makarantun firamare da sakandare, su ne ginshiƙan waɗannan cibiyoyin ilimi. Ta hanyar sadaukarwarsu ga koyarwa da jajircewarsu wajen gudanar da aikinsu, suna gina tunanin ɗalibai, suna kyautata halayensu, tare da dasa musu kwarin gwiwa da ƙwarewar da za su taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen rayuwa.
Su ne abin koyi kuma masu gina al'ummomin gobe. Ta hanyar ƙoƙarinsu ne hauza, jami'a, da sauran makarantu ke ci gaba da cika aikinsu na bunƙasa ilimi, wayewa, da ci gaban al'umma.
Idan hauza da jami'a suka zama wuraren bayar da takardar shaidar karatu kawai ba tare da kyakkyawar manufa ba, za su rasa ruhinsu da martabarsu a matsayin cibiyoyin gina tunani da tarbiyyar al'umma. Hauza da jami'ar da muke fata ita ce wadda ke fitar da mutane masu ɗauke da damuwar al'umma, masu neman mafita ga matsalolinta, kuma masu zama ginshiƙai wajen gina ta, ba nauyi a kanta ba.
Gaisuwa da godiya ga dukkan malamai na hauza, jami'a, firamare da sakandare masu gaskiya, waɗanda ke sadaukar da rayuwarsu wajen gina mutane domin samun ingantacciyar rayuwa da kyakkyawar makoma.
Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka musu da alherin aikinsu a duniya da lahira. Amin.
@Abu Karimat Sambo

Post a Comment