“An Manta Da Mu” – Kukan Shugaban Ƙungiyar Kurame Ta Itas/Gadau Ga Gwamnati Da Ƙungiyoyin Agaji

Daga Wakilinmu, Idris Ibrahim Azare

Shugaban Ƙungiyar Kurame ta Ƙaramar Hukumar Itas/Gadau da ke Jihar Bauchi, Kwamared Abdullahi Saleh, ya bayyana irin mawuyacin halin da kurame ke ciki a yankin, yana mai cewa tsawon shekaru ana ci gaba da nuna musu wariya, ba tare da gwamnati ko mafi yawan masu ruwa da tsaki sun ba su kulawar da ta dace ba.

A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Abdullahi Saleh ya ce, duk da cewa suna da ƙungiyarsu mai suna Itas/Gadau Deaf Association, ƙoƙarin da suke yi na kare haƙƙin kurame da inganta rayuwarsu na fuskantar ƙalubale sakamakon rashin goyon baya daga gwamnati da ’yan siyasa.

Ya ce abin da ya fi damunsa shi ne yadda kurame ke rayuwa tamkar an manta da su gaba ɗaya.

“Mun sha rubuta takardu muna neman a taimaka mana, amma a mafi yawan lokuta ana juya mana baya. Wannan yana sa mu ji kamar ba a ɗauke mu a matsayin cikakkun ’yan ƙasa ba.”

Ilimi Ya Zama Babban Ƙalubale A Gare Mu Da ’Ya’yanmu Kurame

Abdullahi Saleh ya bayyana cewa babu makarantar kurame a Itas/Gadau, haka kuma babu malamai masu iya koyar da yara ta hanyar harshen alamomi (Sign Language), lamarin da ya sa yara kurame da dama suka rasa damar samun ilimi.

Ya bayyana cewa a lokacin tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Itas/Gadau, Abdullahi Muhammad Mai Gari, ya rubuta wasiƙa yana neman a taimaka wajen kai yaran kurame makarantar ilimi ta musamman da ke Yelwa, Bauchi.

A cewarsa, shugaban ya amince cikin gaggawa, aka biya kuɗin rajista da sauran buƙatun yara biyar, sannan aka kai su makaranta.

Sai dai, bayan saukar shugaban daga mulki, tallafin ya tsaya. Rashin kuɗin sufuri da na ciyarwa ya tilasta wa yaran barin makaranta, inda da dama daga cikinsu suka koma yawo a cikin gari ba tare da samun ilimi ba.

Ya ce har yanzu akwai yara kurame masu yawa da ke zaune a gida saboda talauci da rashin makarantar da za su yi karatu.

“Na Yi Karatu, Amma Har Yau Ba Ni Da Aiki”

Shugaban ƙungiyar ya ce ya kammala karatun NCE a fannin Turanci da Hausa daga Kwalejin Ilimi ta Azare a shekarar 2020, amma har yanzu bai samu aikin yi ba.

Ya ce ya nemi aikin gwamnati, ya cika dukkan sharuɗɗan da ake buƙata, amma ba a kira shi ba.

A cewarsa, idan aka ba shi aikin koyarwa a makarantar gwamnati, zai iya tattara yara kurame, ya wayar da kan iyayensu tare da koyar da yaran cikin harshen alamomin kurame, domin su samu damar yin karatu kamar sauran yara.

Haka kuma ya ce idan aka ba shi aiki a Sashen Jin Daɗin Jama’a (Welfare Office) na Ƙaramar Hukumar Itas/Gadau, zai kasance wakilin kurame wajen isar da koke-kokensu ga shugabanni da neman mafita ga matsalolinsu.

Ƙungiyoyin Agaji Ma Sun Manta Da Mu

Abdullahi Saleh ya bayyana cewa tun bayan wata gudummawar da ƙungiyar NAIGAS ta bayar ga wata ɗaliba kurma a shekarar 2020, babu wata ƙungiyar agaji ko hukuma da ta sake kai musu ɗauki.

Ya ce hakan ya ƙara jefa kuramen yankin cikin matsanancin hali, inda da dama ke rayuwa ba tare da ilimi ko sana’o’i ba.

Kira Ga Gwamnati Da Masu Hannu Da Shuni

Shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Bauchi, Hukumar Ƙaramar Hukumar Itas/Gadau, Ma’aikatar Ilimi, Ma’aikatar Jin Daɗin Jama’a, ƙungiyoyin agaji na cikin gida da na ƙasa da ƙasa, da kuma masu hannu da shuni, da su dubi halin da kuramen yankin ke ciki.

Ya buƙaci a samar da makarantar kurame ko a tura malamai masu ilimin harshen alamomi (Sign Language), a ba matasa kurame damar samun aikin yi, sannan a samar musu da wuraren koyon sana’o’i da tallafin rayuwa domin su kasance masu dogaro da kansu.

A Ƙarshe: Kiran Da Ya Kamata A Ji

Kurame ma ’yan ƙasa ne. Suna da haƙƙin samun ilimi, lafiya, aiki da rayuwa mai inganci kamar kowa. Rashin jin magana bai hana mutum baiwa, basira ko ƙwazo ba. Abin da suke buƙata shi ne a ba su dama.

Yanzu lokaci ne da gwamnati, hukumomi, ƙungiyoyin agaji da masu alheri za su nuna cewa ba za a ci gaba da barin wannan rukuni na al’umma a baya ba.

Taimaka wa kurame ba alheri kaɗai ba ne; cika haƙƙinsu ne na ɗan Adam, tare da gina al’umma mai adalci da bai wa kowa dama.

Ko wannan kira zai samu wanda zai amsa? Lokaci ne kaɗai zai bayar da amsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post