An Gudanar da Jana’izar Marigayi Sheikh Usman Kusfa (Rigi-Rigi) a Zariya

An gudanar da jana’izar marigayi Sheikh Usman Kusfa, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi, da yammacin ranar Litinin, 2 ga Fabrairu, 2026, a birnin Zariya, Jihar Kaduna.

Marigayi Sheikh Usman Kusfa ya rasu ne a daren Lahadi bayan ya yi fama da jinya na ɗan lokaci a asibiti. Rasuwar tasa ta janyo alhini da jimami a zukatan al’umma, musamman mabiyansa da ɗalibansa.

Dubban jama’a, maza da mata, ne suka halarci jana’izar, inda Babban Limamin Zazzau, Malam Dalhatu Ƙasim Imam, ya jagoranci sallar jana’izar.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Malam Ahmad Nuhu Bamalli, na daga cikin manyan baki da suka halarci jana’izar domin nuna girmamawa da juyayi ga marigayi malamin.

Bayan kammala jana’izar, an binne marigayin a cikin zawiyyarsa da ke Unguwar Kusfa a Zariya.

Ana addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya masa rahama, Ya kuma sanya Aljannatul Firdausi ce makomarsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post