Hukumar kula da yanayi ta ƙasar Madagascar ta fitar da sanarwar gargaɗi a yankunan da ke arewa maso yammacin ƙasar da ke cikin haɗari daga wata guguwa mai ƙarfin gaske. Ta ce guguwar mai suna Fytia, tana gudun da ya kai kilomita 150 a cikin sa'a guda.
Hukumar ta yi gargadin samun ruwan sama mai ƙarfi da zai haifar da ambaliya da zaftarewar ƙasa da kuma toshe hanyoyi. Madagascar dai na ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya kuma ta na fuskantar barazana daga bala'o'i da ke da alaƙa da yanayi.

Post a Comment