Yan Uwa Fulani Almajiran Sayyid Zakzaky Sun Gudanar da Taron Mauludin Manzon Allah (SAW) a Garin Makarfi, Kaduna



Jiya Lahadi, 30 ga Nuwamba 2025, yan uwa Fulani almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) daga Nana Asama’u Zone, wanda ya haɗa da Zaria, Kaduna, Jos, da Katsina, sun gudanar da taron Mauludin Manzon Allah (SAW) a garin Makarfi, Jihar Kaduna.

Taron ya samu halartar baki daga garuruwa daban-daban, ciki har da Ardo-Ardo da sauran sarakunan Fulani, da matasa daga wurare daban-daban. Sun yi jawabi akan matsayi da martabar Manzon Allah (SAW) da muhimmancin riƙo da karantarwa daga darikar Manzo (SAW) da iyalansa tsarkaka, wadanda suka zama wajibi a riƙa karantarwarsu a al’umma.

Malam Abdulqadir Kudan ya jawo hankalin mahalarta kan wanene Danfodiyo da yadda ake sauya yanayi a yanzu, yana mai gargadin game da maƙiyan addini da ƙoƙarin lalata darikokin Manzo. Haka kuma, ya bayyana cewa Amsakiran Mujaddadin wannan ƙarni, Shehu Magajin Shehu Sayyid Zakzaky (H), shine mafi dacewa wajen jagorantar al’umma, musamman a irin wannan yanayi da ƙasar ke ciki.

Malam Abdullahi Funtuwa ya jaddada gargadi musamman ga Fulani kan irin barna da ake yi wa al’umma a Arewacin ƙasar, inda ya yi kira da a yi hattara sosai domin kare martaba al’umma.

Bayan haka, Malam Husaini Magaji daga Rugan Zakzaky Funtuwa, Malam Abdullahi Welare da tawagarsu sun kawata taron da wasannin al’adu na Fulani da waƙoƙin yabo ga Manzon Allah da iyalansa tsarkaka. An kammala taron lafiya, inda Malam Mika’ilu da wasu yan uwa daga Makarfi suka nuna matuƙar jin daɗinsu da yadda aka gudanar da taron. A ƙarshe, Malam Auwal da Malam Ibrahim sun yi jawabin godiya ga mahalarta da suka halarta.

Post a Comment

Previous Post Next Post