An yi jana'izar fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi ranar Juma'a, wanda ya rasu ranar Alhamis. An yi wa malamin sallah a masallacin Idi na garin Bauchi kafin a binne shi a masallacinsa da ke garin da misalin ƙarfe 6:45.
Wakilin BBC ya ce dandazon mutanen da suka taru a kofar shiga masallacin ta sa sai da jami'an tsaro suka kafa shingaye kafin a iya shigar da shi wurin binnewar. Kazalika, wasu daga cikin iyalansa ba su samu shiga wurin ƙabarin ba saboda cikowar mutanen. Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ne ya jagoranci yi waa malamin sallar jana'iza, kuma an binne shi ne kusa da wasu daga cikin iyalansa da suka rasu a baya.
Sheikh Dahiru wanda jagora ne na darikar Tijjaniyya ya rasu yana da shekaru 98 a kalandar miladiyya, a kalandar Musulunci kuma yana da shekara 100 da ƴan watanni. Shehin malamin ya rasu ne a asibitin sojojin sama da ke jihar Bauchi bayan gajeriyar jinya. Ɗan marigayin, Naziru Dahiru Bauchi, ya faɗa wa BBC cewa an ajiye da gawar shehun a asibitin da ya rasu kafin lokacin da za a yi masa sallah a kuma kai shi makwancinsa.
Naziru Dahiru Bauchi ya ce an tsara yin janaizar ne a ranar Juma'a duk da mahaifin nasa ya rasu ranar Alhamis saboda a bayar da dama ga mutanen da ke nesa su halarci janaizar. Ya ce a cikinsu akwai Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, mutumin da marigayin ya yi wasiyyar shi ne zai yi masa sallah. ''Da ma ya yi wasiyya cewa Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, wanda amininsa ne, shi ne zai yi masa sallah, idan kuma ba ya gari Sheikh Isma'il Khalifa ya yi masa sallah," a cewar Naziru. "Amma Sheikh Isma'il Khalifa ya riga ya rasu."
Ya ce akwai ƴan'uwa da dama da ke nesa waɗanda ake sa ran isowarsu a ranar Alhamis zuwa safiyar yau Juma'a. Naziru ya ƙara da cewa ana sa ran ƴan'uwa da abokan arziƙi da ɗaliban marigayin za su isa Bauchi domin halartar jana'izar daga ƙasashe kamar Canada, da Amurka, da Masar da Saudiyya. ''Wasu kuma sun kira za su zo ne daga ƙasashe makwaftan Najeriya kamar Chadi da Sudan da Kamaru da Benin da kuma Ghana.'' a cewarsa.
Naziru Dahiru Bauchi ya shaida wa BBC cewa mahaifinsa gajeriyar rashin lafiya ya yi, duk da dai a baya yakan yi fama da rashin lafiya saboda yawan shekaru. Ya ce: ''Alhamdulilahi Maulana na samun ƙoshin lafiya. Kullum yakan yi baƙi kuma yakan fito ya karɓe su. Ko shekaran jiya ma ya yi baƙi. Ko a shekaran jiya mutum fiye da 50 ne suka kai masa ziyara.
‘'Kwana biyu ya samu lafiya sosai. A shekaran jiya cikin dare ne jikin ya ɗan tashi aka tafi asibiti. Ana zuwa asibiti kuma rai ya yi halinsa." Naziru ya kuma ce saboda yanayin shekaru, marigayin ya sha fama da larurar saukar jini (Low BP). "Bayan jinin ya sauka a wannan karon, sai ya zo da ajali," in ji shi.

Post a Comment