Lajanar da ke kula da Makarantun Fudiyoyi na Harkar Musulunci a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky a yankin Potiskum ta shirya taron ranar Yara kamar yadda ta saba duk shekara.
Taron wanda ya gudana a garin Potiskum ta Jihar Yobe ya samu halartar ɗunbin ɗalibai da Malamai daga makarantun Fudiyoyin yankin sama da 25.
An fara taron ne a ranar Asabar inda aka gudanar da musabaƙar karatun Alƙur’ani mai girma da kuma wasu wasanni tsakanin ɗaliban. A ranar Lahadi an gabatar da gasar Fareti tsakanin Fudiyoyi guda bakwai da suka fito daga garuruwan: Bulkachuwa, Dagauda, Fika, Gadaka, Buni Yadi, Dawasa da Gashua.
Yayin da ya ke jawabi a wajen wakilin Lajanar Fudiyya na yankin Malam Sadisu Yahuza Potiskum ya bayyana cewar; “Rashin da muka yi na Malam Isma’il, wanda shi ne shugaban Lajnar Fudiyya a wannan yanki ne yasa ba mu yi wannan taron ba sai yanzu.”
Wakilin ‘yan’uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na yankin Potiskum Malam Ibrahim Lawan ne ya yi jawabin rufewa. Malam Ibrahim ya yi addu’a ga ɗaliban da kuma jan hankulansu wajen dagewa da karatu.
Bayan bayyana sakamakon duk kan wasanni da musabaƙar da aka gabatar an kuma bayyana sakamakon Fareti da aka fafata tsakanin Fudiyoyi bakwai inda Fudiyya Gashua ta yi zarra da maki 91.

Post a Comment