Putin: Shawarar Zaman Lafiya ta Amurka Na Iya Zama Tubalin Yarjejeniya a Nan Gaba

 


Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce shawarwarin zaman lafiya da Amurka ta gabatar kan rikicin Ukraine na iya zama tushen yarjejeniya a nan gaba, duk da cewa ba a kai ga matsayar ƙarshe ba tukuna.

Putin ya bayyana cewa Rasha ba ta da wata manufa ta ƙiyayya ga Turai, kuma a shirye take ta tattauna batutuwan da suka shafi tsaron yankin. Ya ce Rasha ta buɗe ƙofa ga tattaunawa kan ƙarfafa zaman lafiya da Amurka.

A cewarsa, dukkan batutuwa da ke cikin shirin zaman lafiya na Ukraine suna bukatar zurfin tattaunawa kafin a samu fahimtar juna. Ya ƙara da cewa ba a kammala shirin zaman lafiya na Amurka ba tukuna, amma Rasha ta yi imanin cewa Washington na la’akari da matsayinta.

Putin ya kuma tabbatar da cewa tawagar Amurka za ta isa Moscow a mako mai zuwa domin ci gaba da tattaunawa.

Game da daftarin shirin zaman lafiya da Ukraine ta gabatar, Putin ya ce yana bukatar a fassara shi zuwa harshen diflomasiyya, domin wasu daga cikin batutuwansa “sun yi kama da marasa ma’ana.”

Dangane da yaki kuwa, Putin ya ce:
“Yaƙin zai tsaya ne idan Ukraine ta janye daga yankunan da aka mamaye a Donbas. Idan ba ta yi haka ba, za mu cimma burinmu ta hanyar soji.”

Post a Comment

Previous Post Next Post