Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari a Ƙaramar Hukumar Dandume A Daren Jiya

A daren jiya Alhamis aka shiga halin tashin hankali da firgici a unguwar Allah Nanan da ke yankin Tumburkai a ƙaramar hukumar Ɗandume ta Jihar Katsina, bayan da wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai suka kai mummunan hari a daren Juma’a.

Shaidu sun bayyana cewa maharan sun mamaye ƙauyen da yawan gaske tare da fara harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya sa mazauna yankin suka fara gudun ceton rai. 

Harbe-harben dai ya ci gaba da gudana na tsawon sa’o’i, ba tare da wata ɗauki daga jami’an tsaro ba, a cewar majiyarmu.

“Muna cikin matsanancin hari. Suna harbin kowa da kowa da suka gani,” in ji wani mazaunin ƙauyen cikin tsoro ta wayar salula kafin layin ya yanke.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto ba a san adadin waɗanda suka mutu ko suka jikkata ba, sai dai jama’a na fargabar cewa akwai waɗanda suka rasa rayukansu saboda irin ƙarfin harbin bindigar da ake ji.

Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar sabon salo na taɓarɓarewar tsaro a sassan jihar Katsina, inda al’ummomin karkara ke fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga da ke cin karensu babu babbaka.

Hukumomi dai ba su fitar da wata sanarwa ba tukunna, kuma ƙoƙarin da aka yi na tuntuɓar jami’an tsaro ya ci tura.

Jama’ar yankin na roƙon gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin daƙile zubar da jini da kuma dawo da zaman lafiya a wannan yanki da ke fama da rikice-rikice.

Post a Comment

Previous Post Next Post