Bayan Kwanaki 126 da Ƙaddamar da Aikin Titi, Har Yanzu Ba a soma ba

*Mazauna Ƙaramar Hukumar Sabon Gari Na Neman A Yi Gaggawar Fara Ayyukan da Aka Yi Watsi da Su

Daga Zailani Mustapha

Fiye da wata huɗu ke nan bayan ƙaddamar da wasu manyan ayyukan gina tituna guda uku a ƙaramar hukumar Sabon Gari da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Jamil Abubakar Albani, ya jagoranta, mazauna yankin sun fara bayyana damuwa kan yadda babu wani ci gaba da aka samu tun daga lokacin.

Ayyukan da aka yi wa laƙabi da “canji na gaske” sun haɗa da: tituna biyu na zuwa da dawowa a daidai gadar sama (flyover) dake Kwangila (Gundumar Hanwa), gada a Palladan (Gundumar Basawa), da kuma titin Sakadadi a Unguwar Dogarawa. 

An ƙaddamar da ayyukan ne a hukumance ranar 16 ga Mayu, 2025, cikin wani biki da ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da ƴan siyasa. Amma har yanzu—kwanaki 126 bayan ƙaddamarwar—babu wani aiki da aka fara a wuraren da aka ambata. Ba a ga ƴan kwangila ba, ko kayan aiki tun bayan da aka kawo su a farkon aikin wanda daga bisani aka kwashe su. Kazalika har yanzu babu wani shiri na a wajen a halin yanzu, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma.

“Wannan ba shi ne cigaban da aka yi mana alƙawari ba,” in ji Ibrahim Sani, wani malami daga Dogarawa. “Sun zo da kamara, da zare-zaren ƙaddamar wa, da kafafen watsa labarai. Tun daga lokacin, ba a ɗora ko sandar aiki ba.”

Da yawan mazauna Sabon Gari da suka zanta da Madogara TV/Radio sun bayyana ƙaddamar war a matsayin siyasa ce kawai da ba ta da tasiri, suna tambayar dalilin wannan alfahari da aka nuna wajen ƙaddamar da ayyukan da ba a da niyyar fara su nan da nan ba.

“Sun yi amfani da shi ne kawai don yaƙin neman zaɓen Uba Sani,” in ji Hadiza Mohammed, wata ‘yar kasuwa a Kwangila. “Mun yi murna, mun yi fatan alheri, amma babu wani canji. Lamarin ma ya ƙara taɓarɓarewa—kurar titi, ramuka, da kuma alƙawuran da ba a cika ba.”

Shuwagabannin al’umma da dama ma sun nuna damuwa, suna cewa irin wannan abu yana karya aminci da ƙwarin gwiwar jama’a ga shugabancin ƙaramar hukuma.

“Idan babu shirin aiwatar da aiki, to me ya kawo wannan yaudara?” in ji Malam Bashir Isyaku, wani matashi jagora a Palladan. “Shugaban ƙaramar hukuma na da hakkin bayani ga mutanen Sabon Gari. Waɗannan ayyuka ba kyauta ba ne—haƙƙin al'umma ne.”

Da aka tuntuɓi wani jami’in ƙaramar hukumar da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa “har yanzu suna jiran ƴan kwangiloli su fara aiki,” amma ya ƙi bayar da lokacin da za a fara ko kuma dalilin jinkirin.

Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Jamilu Albani, ya sha alwashin cewa za a gudanar da ayyukan da gaskiya, riƙon amana, da bin ƙa’idojin inganci. Har ila yau, ya danganta shirin ci gaban da goyon bayansa ga takarar Gwamna Uba Sani a 2027, inda ya ce Sabon Gari “na cikin tsarida hangen nesa na Gwamna.”

Amma yanzu, mazauna Sabon Gari na cewa bai kamata siyasa ta hoto ta maye gurbin ci gaba na ainihi ba, suna kira ga Albani da ya riƙa cika alƙawari. 

Ƙungiyoyin farar hula da masu sharhi na cikin gida sun caccaki wannan jinkiri, suna bayyana shi a matsayin “ƙaddamarwa ba tare da aiwatarwa ba.” Sun ce jama’a sun fi bukatar aiki fiye da ɗaukar hoto da bayyana a talabijin.

“Shugabanci ba ya tsaya da talla ko yaɗa bayanai kawai bane. Aiki ake so,” in ji Barrista Zainab Musa, mai nazarin harkokin gwamnati daga Zariya. “Abin da ke faruwa a Sabon Gari ya zama dole shugabanni su shiga taitayin su. Dole ne su gane cewa ƙaddamar wa ba za ta gina titi ko gada ba.”

Yanzu haka, kira na ƙaruwa ga Hon. Albani da ya cika alƙawarinsa, ya dawo da kwangiloli, kuma a fara aiki cikin gaggawa kan waɗannan ayyuka da jama’a ke jiran su tun da daɗewa.

Har zuwa wannan lokacin, mutanen Sabon Gari na ci gaba da jira—ba sabuwar ƙaddamar wa ba, sai dai ci gaba da gani da ido.

Post a Comment

Previous Post Next Post