Rundunar Matasan Shi'a almajiran El—Zakzaky na garin Jibiya dake Katsina sun gabatar da aikin gayya na gyaran babbar Gada ta garin Jibiya domin taimakon al'umma.
Gadar ta kasance a kan ta ne ake shiga garin Jibiya, amma ƙasa ta taru a samanta har ta kai ga dole sai dai a tsakiyar gadar ake bi, sannan ruwa na kwantawa a kanta sanadiyar toshewar da hanyoyin fitar ruwa suka yi, har abun ya kai yana damun al'ummar garin musamman idan aka yi ruwa.
A yayin aikin al'umma sun nuna jin daɗinsu wajen yin fatan alkhairi da addu'a saboda muhimmanci Gadar.
Tare dayi sheikh zakzaky (H) Fatan Alkhairi

Post a Comment