‘Yan uwan Zamfara Sun je Gaisuwar Ta'aziyyah Ta Rasuwar Sarkin Katsinan Gusau (Sarkin Gusau)

A ranar Lahadi Ne 2 Ga Watan Safar 1447H, Daidai Da 27/7/2025M, Ƴan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibrahim Yaqub Zakzaky (H) Sukaje Gaisuwar Ta'aziyyah Ta Rasuwar Sarkin Katsinan Gusau Wato Marigayi Mai Martaba (Emir Of Gusau) Alh Ibrahim Bello, Wanda Ya Rasu Shekaranjiya Jumu'a, Sheikh Abubakar Nuhu T/Mafara (Malam Abba) Ne Ya Jagoranci Tawagar Ƴan uwa Zuwa Wajen Ta'aziyyar, Gaisuwar Ta Haɗa Da Ƴan uwa Na Gusau, Tsafe Da Sauransu. 

Yayin Jawabin Sheikh Abba Bayan Yayi Gaisuwa Ga Masarauta Sannan Yace Mu Munzo Ne Amadadin Ƴan uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Yaqub Zakzaky (H) Na Zamfara, Daga Ƙarshe Sai Akayi Addu'a Ta Musamman Ga Marigayin, Muna Roƙon Allah (SWT) Ya Jiƙansa Da Rahmah, Mu Kuma Idan Tamu Tazo Allah (SWT) Yasa Mucika Da Imani. 

Post a Comment

Previous Post Next Post