Yadda Bikin Murnar zagayowar Ranar Auran Imam Ali Da Sayyida Fatimaz Zahara (AS) Ya Gudana A Garin Zariya

 

Ƴan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky na Da'irar da kewaye sun gudanar da gagarumin taron murnar zagayowar ranar Auran Sayyida Fatimaz Zahara Da Imamu Ali (AS) a yau Alhamis 29 ga watan Mayu, 2025 a Muhallin Fudiyyah da ke cikin birnin Zariya.

Ƴan uwa na na harkar Musulunci yankin Zariya ne suka jagoranci gabatar da taron, ya sami halartar al'umma daban-daban na yankin Zariya da kewaye.

Taron ya sami baƙwancin Shugaban Makarantar koyar da ilimin harshen Turanci ta (Elsa) inda ya gabatar da jawabi na musamman akan muhimmancin wannan rana mai matukar daraja.

Mai Elsa ya gabatar jawabi a karkashin maudu'i mai taken "koma bayan da ake samu dangane da zamantakewar aure laifin wane ne"? sau kuma "Zamantakewar aure juya da yau ta ina ne aka gaza da ya sa muka kasa cimma iyayenmu". "suwane ne Maza Sannan kuma wace ce mace. (a wasu lokutan rashin sanin juna na kawo koma baya zamantakewa)

ya fara da cewa auren Sayyida Zahara da Imam Ali (AS) ya na nuna abubuwa ne da yawa. wane ne Imam Ali, wane ne kuma Fatima.

Ya kuma yi tsokaci kan auran Sayyida Zahara Da Imamu Ali inda ya yi tsokaci tun daga kan auran tare da maneman da suka zo neman auratan kana ya bayya hikimar Ubangiji da ya zama Imam Ali (AS) ne ya zama mijinta.

Daga karshe, Malam Mai Elsa ya yi kira ga ma'aurata da su yi koyi da yadda zaman takewar Sayyida Zahara da Imam Ali (AS) ya bayyana "hakan zai kawo sauye-suyen mai amfani a cikin zaman takewar".

Tun da farko Bayan buɗe taron da addu'a da karatun Alqur'ani Mai Girma, Mawaka Harkar Musulunci, Sani Ɗan Aura da Ammar Ɗan Rinka sun gabatar da wakokin yabo na musamman da suka shafi wannan munasaba. Inda suka nishaɗantar kuma suka ilmantar.

Kana da karshe, Malama Amina Sulaiman Bawa ta gabatar da jawabi a takaice dangane da yau dara da ake samu a tsakanin mata da maza yayin kulla alakar soyayya.

Wakilin ƴan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky na Da'irar Zariya, Shaikh Abdulhamid Bello ya gabatar da ta'alikinsa a takaice, daga karshe bayan kammalawarsa aka yi addu'a aka sallami kowa.

© Zaria Media Forum
29052025

Post a Comment

Previous Post Next Post