Wata babbar kotu a Legas ta samu wani direban motar bas, Andrew Ominikoron da laifi, tare da yanke masa hukuncin kisa, kan kisan wata budurwa mai shekara 22, Bamise Ayanwola. A zaman kotun na sama da awa biyu da rabi, mai shari'a Serifat Sonaike ta ce kotun ta tabbatar, ba tare da wani shakku ba cewa mutumin shi ne ya aikata laifin. Daga nan sai mai shari'ar ta furta cewa "za a rataye ka har sai ka mutu a matsayin hukunci kan kisan da ka yi wa Oluwabamise Ayanwola."
Duk da cewa babu wani da ya shaida yadda lamarin ya faru, kotun ta dogara ne da bayani kan abubuwan da suka faru, da bayanin likita da kuma bayanan da wadda aka kashe ta yi gabanin mutuwarta. Kisan da aka yi wa budurwar, Bamiseye a shekarar 2022 ya fusata al'umma tare da janyo tofin Allah tsine, lamarin da ya sanya shari'ar ta É—auki hankalin al'umma.
Kotu ta ce direban ya yi ƙaurin suna wajen ɗiban fasinja ba bisa ƙa'ida bayan lokacin tashi aiki, inda yakan kashe wutar cikin motar, ya kulle ƙofofi sannan ya aiwatar da aika-aika. Kotun ta ƙara da cewa direban ya fi yi wa mata masu ƙananan shekaru irin wannan ta'asa, inda yakan ɗauke su zuwa wajen da babu wanda zai cece su, inda yakan yi musu fyaɗe. Yakan sadu da su ba da amincewarsu ba, in ji kotu.

Post a Comment