NAPTIP ta kuɓutar da ƴan Najeriya tara da aka yi niyyar safarar su zuwa Libya



Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane ta Najeriya, NAPTIP ta ce ta kuɓutar da wasu ƴan Najeriya da aka yi niyyar safararsu zuwa Libya.

Kwamandan hukumar a jihar Zamfara, Aliyu Abubakar ya bayyana cewa an samu nasarar ceto mutanen tara ne a iyakar Babura da ke jihar Jigawa, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Najeriya ya ruwaito.

Aliyu ya ce akwai mata guda uku cikin mutanen tara - waɗanda ƴan asalin jihar Zamfara ne.

Sun tserewa gidajensu ne sakamakon hare-haren ƴanbindiga, inda suka koma zama a Kaduna.

NAPTIP ta ja hankalin mutane kan faɗawa makomar masu safarar mutane - inda ta ce kowa ya yi taka tsantsan.

Safarar mutane dai ba sabon abu bane a kan iyakokin Najeriya, inda a watan Fabrairu, gwamnatin jihar Neja ta karɓi yara 21 da hukumar shige da fice ta kuɓutar da su - waɗanda ba su haura shekara tara ba lokacin da ake tafiya da su Nijar.

Post a Comment

Previous Post Next Post