Daga Garin Karbala Kasar Iraki: An Gudanar Da Zaman Juyayin Shahadar Imam Ali


An gudanar  da shan ruwa tare da zaman makokin shahadar Imam Ali AS a gidan Buhari Mustapha Sambo dake Karbala. Sheikh Ayub Adam Zariya ya gabatar da Sheikh Junaidu wakilin ‘yan’uwa na garin Kudan ya yi jawabi. 

A jawabin na shi ya tabo tarihin gwagwarmayar Imam Ali AS wanda ya yi bayan wafatin Manzon Allah (SAW) kamar yaʙin Siffeen da abuwawan da ya faru a wurin. 

Kuma daga nan ya yi bayanin yadda Ibnu Muljam ya sari Imam Ali (AS) a kai da kuma wasiyyar da Imam Ali AS ya yi ga Imam Hasan (AS). 

Bayan gama jawabin, Dr Ibrahim Adam Wushishi ya yi ta'aliki akai sannan Sidi Kabeer Kaduna ya rufe taro da addu'a.

Post a Comment

Previous Post Next Post