Daga Mardiyya Kabiru
A ranar Lahadi 09/02/2025 Dandalin matasan Harkar musulunci, almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na garin Bomo suka shirya gagarumin Mauludin Imam Aliy Bin Abu Talib (AS). An fara da bude taro da addu’a sai kuma karatun Alkur'ani daga Mardiyya Sa'eed sai ziyarar Imam Aliy (AS) wacce Mardiyya Saleh ta karanta. Ittahadu Shu'ara suma sun nuna na su soyyayar ga shugaban Muminai Iman Aliy (AS) ta hanyar wake shi da suka yi da gwalagwalan baitoci.
Sai daga bisani Malam Alhassan Yahya ya kawo mana wasu darajoji na Imam Ali (as) a cikin Alkur'ani da Hadisai. Inda ya ce; Manzon Allah (S) yana cewa, lallai ni mai wa'azantarwa ne kuma kowacce al'ummar tana da mai shiryatar da ita inda Manzon Allah yake nuni da cewa Imam Aliy mai shiryatarwa_duk a cikin darajojin Imam Aliy wanda Alhassan Yahya ya jagoranta kawo shi.
Sai jawabi daga bakin Malama Hafsat Jushi wacce Khadija Abdullahi ta gabatar da ita. Daga cikin jawabin malamar ta bayyana cewa bayan Manzon Allah babu wanda ya kai Imam Ali ilmi saboda ya sha ilimin ne a wajen Manzon Allah (S) inda ya zama Manzon Allah ne gidan ilmi Aliy ne kofar shigarta. Addini bai tsaya da kafarsa ba face da tsayuwar Imam Aliy dan Abu Talib (as) inda ya zama jarumin da babu kamarsa ta yadda yazama garkuwa ga addinin musulunci gaba daya. Imam Aliy shi ne ya zama jarumin da ya fanshi ran Manzon Allah (SAWW) lokacin da mutanen Makkah suka shirya su kashe Manzon Allah inda ya yarda ya kwanta akan gadon Manzon Allah (S) a daren hijra.
Da Itace da duwatsu za su zama abin rubutu to sun yi kadan su rubuta yawan darajojin da Imam Aliy yake da shi. Idan kan aso kaga Al'kurani a aikace to ka yi duba zuwa ga Aliyu Dan Abu Talib (AS). Kadan daga cikin jawabin da Malamar ta gabatar ke nan a wajen taron. Sai yanka Alkaki wanda Malam Aliyu Dalhatu Bomo ya jagoranta. Sai rufe taro da addu’a wacce babbar malamar ta rufe taron
~FMB PRESS HAUSA~
Post a Comment