AN GABATAR DA MAULIDIN NISFUS SHA'A BAN A GARIN BOMO DAKE KARAMAR HUKUMAR SABON GARI


Daga Mansur Kabiru 

An gabatar da gagarumin mauludin NUSFU SHA'ABAN a garin Bomo Wanda Mal. Auwal gashuwa  Ya gabatar. Daga cikin jawaban na mal ya fara da bayani akan godiya ga ni'imar da Allah yayi Dan Adam. Sannan Mal ya Kara da cewa Babu wata ni'imar da Allah yayi ma Dan Adam face imani.  Sannan Mal yayi magana akan Wani kissa wanda Manzon Rahma yake cema sayyada Fatima (A.S) da cewa imam Mahdi (AJF) yana cikin 'yayanta 

Haka lazalika wata rana Manzon Allah suna tafiya tare da imam Ali yake tayashi murna cewa Mahdi (AJF) yana daga cikin 'yayansa. Sannan wata rana imam Hussain Yana tare da Manzon Rahma yake cewa wannan addini bazai gushe ba sai wannan imamai sha biyu sun halarta sannan na karken nasu shine Iman Mahdi (AJF) sannan Yana daga cikin 'yayan Hussain. Mal ya Kara dacewa akwai hadisai sama da dubu biyar akan zuwa imam Mahdi(AJF). 

Daga cikin jawaban na mal ya kawo cewa Allah zai daukar iyalen Manzon Allah fasa ta hanyar dawo da shugabanshi a hannu su ta hanyar imam Mahdi (AJF) sannan wannan sakon Allah ya rubutashi a zaburan Annabi Daud da Kuma injila sun kawo zuwa imam Mahdi (AJF). Sannan su wannan azzlumai sun san cewa akwai Mai gyara ko mai tsawatar wa yananan zuwa wato Mahdi (AJF). Daga ciki Allah (SWT)  ya kawo cewa Babu Wanda zai yadda da zuwan Mahdi (AJF) sai Mai imani. Sannan ALLAH yayi Imam  Mahdi (AJF) tanadi Mai girma saboda mahaifin imam Mahdi (AJF) ya rayu a kurkuku Mai suna Samarra saboda su azzalumai sun San cewa imam Mahdi AJF zaizo daga imam Hassan Al'askari lokacin da Allah ya shirya zuwan imam Mahdi (AJF) a duniya, ba mahaifin imam ya samu mahaifiyarsa ba Wani alamari ne ya faru,  mahaifin imam Hassan Al'askari (AS) wato imam Ali al-hadi shiya aika Mai mashi hidima Cewa za'a zo da wata baiwa da aka ciwo a wani yaki mai sufa da irin Wanda imam Ali al-hadi (AS) ya kwatanta mashi. Kuma haka ya ganta kamar yarda imam yayi mashi nuni akan sufar ta. Lokaci da ciniki ya fada sai wannan baiwar ta fara dariya sai wannan Dan Sako yake tambaya dariyan me take? Sai take cewa lokacin zuwa gurin shugaba yayi shiyasa take murna.  Sannan aure mahaifar imam Mahdi AJF anyi aure tun kafin makiya sunan cewa za'ayi auren.  

Sannan lokacin samuwar imam Mahdi (AJF) bayan hijira da shekara 250 a watan shaaban a rana ta ana gobe Nusfu shaaban. A irin wannan lokacin imam Hassan Al'askari yake fada goggonsa wato hakima sai yake cewa ya umma a yau daren nan Kisha ruwa a gidan nan saboda gidan nasu da nisa, sai take tambayansa me dalilin da zansha ruwa a gidaka  imam Hassan Al'askari (AS) yake cewa a wannan daren ne Allah (SWT) zai kawo Mai gyaran duniya nan lokacin zuwansa yayi sai take tambaya wa zai haifesa imam Hassan Al'askari (AS) yake cewa Narjis ce zata haifesa.  

Sai hakima take cewa ai bataga alama ba. Imam Hassan Al'askari wannan alamari Allah (SWT) shikenan sai hakima ta zauna ba tare da Wani ko kwanto ba akan alamari Allah (SWT) bayan haihuwar imam Mahdi (AJF) sai mahaifisa ya huduba. Daganan imam Mahdi (AJF) yayi girman da kowa yayi mamakin girman nasa daganan sai makiya suka samu labarin haihuwar nasa sai suka fara Shirin kisa na imam Mahdi (AJF). An sanya mashi guba Amma baa samu nasaran kashe shi ba.  Daga Karshe anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post