A Ranar Lahadi 16 ga watan Fabrairu 2025 aka gudanar da taron ranar Taklifi ga yara wanda suka kai shekarun Balaga, kuma taron ya gudana ne a Hussainiyyatu Sheikh Zakzaky (H) Jos.
An fara da yiwa yara karatu akan taklifi da kuma wajibci akan musulunci, sannan kuma aka fara karanta musu abin da yake cikin littafin da aka raba musu. An karantar da su yadda ake yin wankan janaba ga maza, sannan kuma suma mata aka karantar dasu yadda ake wankan haila wanda Malama Maimuna da Mujeebah Aljasawi suka koyar dasu tare da nuna musu yadda ake yi.
An nuna musu yadda ake yin alwala da kuma yin taimama idan ba'a sami ruwa ba, ko kuma idan mutum yana da wani ciwo a jikin shi wanda bazai iya yin amfani da ruwa ba, to wannan zai iya yin amfani da kasa yayi taimama.
An kuma nuna musu yadda zasu yi taimama da kuma irin kasar da zasu yi amfani dashi yayin yin taimama din misali kamar; Turɓaya, Yashi (rairaiyi), busassiyar ƙasar tukunya da dai sauransu. Sannan an faɗa musu hukunce hukuncen taimama din.
1. Wajibi ne shafar goshi, shafar ta kasance da dukan cikar hannuwan biyu, wato har da cikin yatsunsu.
2. Wajibi ne a gusar da duk wani abu da zai hana a shafi fatar jiki, kamar fenti da zobe.
3. Abubuwan da suke bata alwala su ne ainahin abubuwan da suke bata taimama.
Bayan an kammala nuna musu yadda ake yin taimama sannan kuma aka kira wasu daga cikinsu domin su yi yadda aka nuna musu, kuma sun yi yadda aka nuna musu din.
Wakilin yan uwa na Jos Malam Auwal Gangare ya jagoranci Yaran Takalif ɗin Sallah, daga ƙarshe yayi jawabin kammalawa wanda yayi bayani akan yadda ake yin sallah da kuma yadda zasu kula da wajibansu, ya kuma ja musu kunne akan idan har sunyi ba daidai ba ko kuma sun sabawa Allah, Allah zai hukumta su.
#everyone
#highlights
YOUTH FORUM MEDIA TEAM JOS
16-Feb-2025
Post a Comment