Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da wasu daga cikin ƴan uwansa na jini, waɗanda suka kawo mishi ziyara daga Sabon Garin Gabas, dake yankin Zariya, a gidansa dake Abuja, da yammacin yau Lahadi.
A yayin ganawar Jagora (H) sun yi hira da maziyartan cike da raha, da nasihohi gare su kan kiyaye haƙƙin ƴan uwantaka da kuma sada zumunci, inda ya bayyana musu cewa, ba kakanninsa kaɗai yake yiwa addu'a ba, hatta zuri'arsu duk ya na sanya su cikin addu'a, saboda haƙƙin iyayensa a kansa.
Bayan gabatar da Sallah Maghriba da Isha'i Jagora ya gabatar da kyautuka gare su, sannan aka yi bankwana tare da fatan Allah ya maida su gida lafiya.
@SzakzakyOffice
#EidMobarak
#ShaabanKareem
#PrayForPalestine #OurMartysOurHeroes
17/Shaaban/1446
16/02/2025
Post a Comment