Alhamdulillah!
A yau na samu zuwa asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello dake Shika (ABUTH Shika) domin duba marasa lafiya da gaishe-gaishe, inda na duba jikin Malam Ashiru Talba da Anas Cho-boy da yarinyar Umar Unguwan Rimi wanda suke kwance a wannan asibiti.
Daga nan na zarce gundumar jama'a don yin ta'aziyya ga iyalan marigayi Hussaini Gamawa wanda Allah Ya yiwa rasuwa kwanakin baya da kuma iyalan Alh. Abdu Idris da kuma Dr. Tasi'u dake garin Palladan.
Sannan na Wuce Zabi gidan sarkin Zabi don yin ta'aziyya da kuma ta'aziyyar Alh. Dauda Mai Itace dake unguwan Jebbah da Mal. Sunusi Dillali dana marigayi Mal. Dandodo mai shayi, Dogon Bauchi.
Nayi addu'an Allah Ya jaddada rahama agare ga wadannan bayin Allah , su Kuma iyalai Allah Ya basu hakurin jure wannan rashi.
Suma marasa lafiya nayi addu'an Allah Ya basu lafiya mai daurewa tare da sauran al'ummar da suke fama da jinya gaba daya.
Hon. Sadiq Ango Abdullahi
Member, Representing Sabon Gari Federal Constituency
Deputy Chairman, House Committee on FERMA
2nd January, 2025
Post a Comment