Jagora Sayyid Zakzaky (h) Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Marhuma Malama Fatima (Binta) Abdullahi



A ranar Talata da ta gabata (17/12/2024) ne Jagoran Harkar Musulunci As-Sayyid Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky (H) ya yi ta’aziyya ga Shaikh Yakub Yahya Katsina na rasuwar babbar Matarsa Marhuma Malama Fatima (Binta) Abdullahi.

Jagora (H) ya gabatar da wannan ta’aziyya ne ta hanyar kiran waya wadda ta gudana misalin ƙarfe 9 na dare. Bayan ta’aziyyar Jagora (H) ya yi addu’o’i ga Marhuma. Har wayau a cikin zantawarsu, Sayyid (H) ya tambayi adadin ’ya’yanta da jikoki da kuma shekarun da suka ɗauka a tare da Shaikh Yakub.

Marhuma Fatima wadda aka fi sani da Malama Binta, sun kwashe tsawon shekaru 50 da aure tare da Shaikh Yakub, kuma sun haifi aƙalla 10, da jikoki 41 da tattaɓa kunne 5, kamar yadda Shaikh Yakub ɗin ya sanar da Sayyid Zakzaky (H) a wayar tarho.

#الفاتحة 

#البقاءلله 

#18_12_2024m 

Shaikh Yakub Yahya Katsina

Post a Comment

Previous Post Next Post