Daga Mansur Kabiru
A ranar Talata 24/12/2024 aka gabatar da maulud na Manzon Rahma Muhammad SAWW a wata ruga Mai suna Rimin Doka. An gabatar da da addu'oi sai karatun Qur'ani daganan sai Mal. Abdulhamid Zubair ya gabatar da takaitaccen jawabi daganan, bayan nan sai wakilin yan uwa na wanka Mal.aYunus wanka ya gabatar da Mai jawabin maulud wato Mal. MUSA TUDUN WADA ZARIA Wanda yayi jawabai masu ratsa jiki a Manzon Allah yayi magana akan rayuwa na Manzon Allah SAWW da Kuma dabi'un sa da Kuma baiwa da Allah SWT yayi masa sannan ya tabo janubin Al'ummar da Kuma matakin dangane da rayuwan Manzon Allah SAWW a cikin jawaban nasa na tabo rayuwan Al'ummar Fulani da martaba da daukaka da daraja da Allah SWT yayi Al'ummar Fulani sannan ya jawo hankalin akan sun Al'ummar Fulani da kar suyi Sakacin zubar da mutuncin su da baiwa da Allah SWT yayi masu da daukaka irin na addini musulunci ya Kuma jawo hankalin ga sauran Al'ummar da kar makiya suyi amfani da abinda suke Yi domin raba kan Al'umma musamman hausa Fulani da irin tarko da makircin da ake ci na makiya
anyi mauludin lafiya an tashi lafiya.
-FMB PRESS HAUSA

Post a Comment