Daga Mansur Kabiru
A ranar Alhamis 26/12/2024 aka gudanar gagarumin mauludin sayyada Zahra (AS) Mai taken suna: ALLAH (SWT) ZAI YI MAULUDIN SAYYADA ZAHRA (AS) A ALJANNA . An fara da bude taro da addua sai Kuma karatun Qur'ani daga Mardiyya Saleh sai Kuma ziyarar sayyada Zahra (AS) wanda Mardiyyah Saeed ta karanto Daga nan sai majalisin sha'irai sai Kuma display Wanda Daliban fudiyya suka kawo sunayen sayyada Zahra (AS) gabatar inda suka kawo darajar sayyada Zahra (AS). Sai gabatar da Mai jawabi Wanda wakilin yan uwa na samaru Mal Muhammad Barau samaru ya gabatar da Mai jawabi Mal Aliyu Turmizi Kaduna. Daga cikin jawaban na Mal. Aliyu Turmizi
Ya fara da gaisuwa irin ta addini musulunci sannan ya nuna farin cikin sa da Allah (SWT) ya kawo mu ranar ta haihuwar sayyada Zahra (AS ) sannan ya Kara da cewa soyayyar sayyada Zahra (AS) kogi ne. Sannan Yace akwai ranar da Allah SWT zaiyi mauludin sayyada a aljanna. Malam ya Kara da cewa makiya so suke su boye sunan da darajar gidan Annabi dana yaransa.
Mal. Yana cewa Allah (SWT) ranar kiyama zai ware masoya sayyada Zahra AS da Kuma makiyanta Mal yana cewa a irin wannan Taron ne ake fadin wacece Sayyada Zahra AS domin samun uzuri gurin Allah (SWT). Mal yane cewa idan baka bi sayyada Zahra AS addininka bai cika ba sannan Yace duk littatafan sunan sun kawo darajar sayyada Zahra (AS).
Mal. ya kawo kissa na samuwar sayyada Zahra daga wasi sassa na itatuwan Aljanna Kuma daga cikin daraja na sayyada Zahra AS shine tun tana ciki take fira da mahaifiyata. Yana cewa lokacin da cikin sayyada Nana Khadija ya isa haihuwa ta fara nakuda tayi kira ga mutanen makka dasu taimaka Mata suyi mata unguwar zoma sai suka nuna cewar tinda ta auri Dan Abdullahi to bazasu taimaketa shine Allah ya Aiko matan aljanna guda hudu domin su taimaka Mata daga ciki akwai
1-Asiya matar fir'auna
2-Saratu
3-Ummu khursum
4-Ummu uktu musa

Post a Comment