FAALALAR SALLAR JAM'I
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalinsa ya ce: Babu wani mumini da zai yi tafiya zuwa ga sallar jam’i face sai Allah Ta’ala ya saukaka masa firgicin ranar kiyama sannan ya saka masa da Aljanna. (wato Allah zai sa shi a cikin aljanna).
Daga Cikin Littafin Khisal na Sheikh Suduq.
- Abu Kareemah Sambo
SAYYID ALI KHAMNE’I
Sahayonawa wawaye suna faɗaɗa bangaren gwagwarmaya neda da hannayensu
Laifukan da yahudawan sahyoniya suke aikatawa ko a Lebanon ko a Gaza da Palastinu suna haifar da sabanin abin da suke so wato suna karfafa tsayin daka da kuma kara karfin (’yan gwagwarmaya). Matashin Bafalasdine mai kishi da kuma matashin dan kasar Lebanon mai kishin sun gane cewa akwai hadari, ko suna fagen fama ko a'a; A don haka sai ya ga ba shi da wani zabi, sai ya ce: Mu je wajen yin arangama (mukawama). Kuna ƙarfafa shi ya yi hakan. Waɗannan wawaye suna faɗaɗa dakewa da juriya da hannayensu.
Imam Khamene'i "Inuwarsa ta tabbata" a wata ganawa da masu fafutuka | 11/25/2024
Post a Comment