Haramin Imam Husaini Ya Tuna Da Shahadar Al-siddiqa Al-zahra A Karbala



Babban Sakatariyar Haramin Husaini ta gudanar da taron  zagayowar ranar shahadar Fatima Al-Zahra, tsira da amincin Allah su tabbata a gare ta, a dakin taro na makarantar Imam Husaini, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a Masallacin Imam Husaini. 

An gudanar da taron juyayin ne a gaban shugaban sashen kula da harkokin addini Sheikh Ahmed Al-Safi, da shugabanin sassa da dama, da kuma babban taron muminai na juyayin Limamin Zamani, Allah ya gaggauta dawowar sa mai girma, kan wannan kunci na mahaifiyarsa Al-Zahra amincin Allah ya tabbata a gare ta. Taron juyayin ya soma da karanto wasu ayoyin Allah ta'ala. 

Daga nan sai Shehin Malami, Sheikh Saeed Al-Sari ya hau kan mumbari, inda a cikin karatunsa ya yi jawabi mai ratsa zukata dangane da Sayyida Zahra da rayuwarta, tare da yin bayani kan cutarwar da ya same ta bayan wafatin mahaifinta Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka.

Post a Comment

Previous Post Next Post