Ta'addancin haramtacciyar kasar Isra'ila a kasar Lebanon da dubbanin mutane suka rasa muhallinsu na kwana a wannan yanayin kungiyoyin addinin musulunci da malaman Musulunci sun fara kai kayan agaji na kayan da ake amfani da shi lokacin sanyi hakan ya biyo baya ne saboda kiran da kungiyoyin da suke kula da wadanda suka rasa mutsuguninsu akan taimaka masu saboda shigowan sanyi mutane suna cikin yanayi mara dadi.
Kuma wannan tallafi na agajin kayan sanyi kamar abin rufa da sauran su sun fara isa hannun wadanda ake taimakawa kamar yadda daya daga cikin kungiyoyin da suke kula da su ya bayyana.
Ita haramtacciyar Isra'ila ta kwashe shekaru masu yawa tana kai munanan hare-haren ta'addanci a cikin kasar Lebanon da kuma kasar Falasɗinu. Ita haramtacciyar Isra'ila tana mamayan kasar Falasɗinu da gina ma Yahudawa 'yan kama wuri zauna gidaje kuma haramtacciyar Isra'ila tana samun goyon bayan daga kasar Amurka da wasu manyan kasashen duniya kamar Ingila da Faransa da sauran su

Post a Comment