A ranar Talata ne 'yan'uwa almajiran Sayyed Ibraheem Zakzaky (H) na Unguwan Maigamo dake karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna suka shirya gagarumin maulidin Manzon Allah (SAWW) wanda suka saba shiryawa a duk shekara.
Bayan bude taro da addu'a, sai karatun Alkur'ani mai girma. Daga nan 'yan tamsiliyyah suka gabatar da tamsiliyyah mai dauke da darasin halin da muke ciki na tsadar rayuwa. Sai kuma 'display' da rundunar Sayyed Humaid wato 'Yan Firqatu Humaid suka gabatar. Sa'annan matasan Harisawa kuma suka yi ziyara. Bayan nan 'yan fareti suka kara kawata wajen.
Daga Nan sai Babban malami mai Jawabi Sheikh Abdullahi Zango, ya fara da gwala-gwalan jawabi akan rayuwar Manzon Allah (SAWW) wanda ya zamo abin koyi. Shehin Malamin yana cewa; Manzon Allah (SAWW) ya ce duk wanda ya yi sallah ba tare da ya yi mani salati ba to hakika sallarsa ta baci. Manzon Allah (SAWW) ya ce ku so Allah saboda ni'imomin da ya yi agare ku sannan ku so Annabi saboda Allah sannan ku so iyalan gidansa (Ahlulbait) saboda Annabi Muhammad (SAWW).
Sannan ya ci gaba da yin jawabi a kan masa'ib din da suka faru da Iyalan Gidan Manzon Allah (SAWW) don duk saboda al'ummah su fahinci darajojin da suke da shi. Manzon Allah ya zama ma al'umma madubi ne a kan ayyukansu wajen koyi da rayuwarsa kamar yadda Shehin Malamin ya yi bayani.
Post a Comment