Mataimakin Shugaban Sha’ari’a na Farko a Iran ya yi kira da a rubuta asarar da ƙasar ta fuskanta sakamakon yaƙin da aka dannawa Iran, sannan a shigar da ƙara kan ƙungiyar Sihiyona da Amurka a gaban kotunan duniya.
Yayin da yake bayyana wajibcin bin diddigin laifukan da ƙungiyar Sihiyona da Amurka suka aikata a dandalan shari’a na ƙasa da ƙasa, Hojjatoleslam Khalili ya ce Mataki na 2 na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya ya haramta amfani da ƙarfi ko barazanar amfani da shi kan mutuncin yanki da 'yancin siyasar kowace ƙasa.
Ya ce, an tilasta wa Iran shiga yaƙi wanda a fili yake nuna zalunci ga ƙasar. Don haka, bisa ƙa’idoji da dokokin kasa da kasa, ƙasar da ta aikata hakan tana da alhakin biyan diyya.
Mataimakin Shugaban Sha’ari’a na Farko ya kuma bayyana cewa, manufar taron da suka gudanar ita ce kafa hanyoyi da tsare-tsaren shari’a domin shigar da ƙara a kotunan cikin gida da na ƙasashen waje.
Ya ƙara da cewa taron zai tantance fannoni na doka da shari’a game da ayyukan ta’addancin da ƙungiyar Sihiyona da Amurka suka aikata, tare da halartar hukumomi da jami’an tsarin shari’a, domin samar da daftarin ƙara mai cikakken tsari da ƙa’ida.
Ya jaddada cewa wannan aiki na shari’a yana buƙatar haɗin gwiwa tsakanin sassan doka, zartarwa da shari’a. Ya ce wajibi ne a kare haƙƙin jama’a da kuma tabbatar da cewa wadanda abin ya shafa sun amfana daga tsarin shari’a.
Haka kuma, ya ce Ma’aikatar Harkokin Waje da Ofishin Shari’a na Fadar Shugaban Ƙasa ya kamata su rubuta adadin asarar da yaƙin da aka sanya ya jawo, sannan su kai ƙara kan ƙungiyar Sihiyona da Amurka a gaban kotunan duniya. Ya ce kafa kwamiti na musamman don tattara bayanan asarar zai taimaka wajen bin diddigin lamarin.
Ya yi nuni da cewa, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada muhimmancin bi da ƙarfi wajen bin diddigin zaluncin Isra’ila da Amurka a kotunan cikin gida da na duniya, inda ya ce wannan batu ba ya bukatar sakaci. Hukumar shari’a ta ce ta riga ta fara aiwatar da aikin da himma, kuma za ta ci gaba har sai an kai ga sakamako.

Post a Comment